#Arewanews
11 Janairu, 2022
Daga: Muhammad Abdallah
KADUNA, NAJERIYA - Ƙaramar hukumar Giwa na daga cikin yankunan da ke fama da matsalar hare-haren 'yan fashin daji a jihar Kaduna.
Gwamnatin jihar Kaduna da ke arewa maso yammacin Najeriya ta ce dakarun kasar sun dakile wani hari da ɓarayi suka yi niyyar kai wa a Kwanar Bataro da ke karamar hukumar Giwa.
Hukumomin jihar sun kashe ‘yan ta’adda biyar.
Wata sanarwa da Kwamishinan tsaron cikin gida Samuel Aruwan ya fitar ta ce sojojin suna aikin sintiri ne a yankin na Giwa a lokacin da suka samu bayanan sirri da ke cewa ‘yan ta’addan sun nufi garin da ake kira Fatika.
Sun ƙara da cewa,
“Hakan ya sa dakarun suka ɗunguma zuwa yankin Marke da Ruheya don kai ɗauki.”
Ya ƙara da cewa,
“A lokacin da tsagerun suka hango dakarun, sai suka nemi tserewa. Amma sai sojojin suka yi musu ƙofar rago a yankin Kwanan Bataro inda aka yi musayar wuta, a sanadiyyar hakan biyar daga cikin ‘yan ta’addan suka mutu.”
Gwamna Malam Nasiru El Rufai ya yi matuƙar farin ciki da wannan nasara inda ya jinjinawa sojojin ƙasar kan matakin da suka ɗauka na gaggawa wajen kai ɗauki.
Yankin ƙaramar hukumar na Giwa n fama da matsalar hare-haren ‘yan fashin daji, waɗanda a baya-bayan nan suka kashe mutum sama da 30 a harin da suka kai wasu ƙauyuka da ke yankin.
Garuruwan Katsina da Kaduna da Zamfara da Sokoto da Kebbi na fama da hare-haren ɓarayin daji.
Wasu Rahotanni
0 Comments