Talla

An kama wanda ake zargi da yi wa Tsohuwa fyade a Nasarawa

 Daga: Muhammad Abdallah

BAUCHI, NAJERIYA - An kama wani da ake zargin ya yiwa wata tsohuwa ƴar shekara tamanin 80 fyaɗe a Jihar Nasarawa.

Rundunar 'yan sandan Jihar Nasarawa da ke Arewacin Najeriya ta ce ta kama wani mutum mai shekara 43 bisa zargin yi wa wata tsohuwa ƴar shekara 80 fyade. 

Ta bakin Mai magana da yawun rundunar wato Ramhan Nansel, a wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi ya tabbatar da kama mutumin.

A cewar sanarwar, a ranar 14 ga watan Janairun nan ne aka shigar da ƙorafin cewa wani mutum mai suna Ɗanasabe Eddo ya yi wa tsohuwar fyaɗe, an shigae da ƙorafin ne a ofishin 'yan sanda da ke Garaku. Wanda ake zargin wato ɗanasabe ɗan asalin jihar Kaduna ne amma yana zaune a ƙauyen na Garaku da ke ƙaramar hukumar Garaku. Mutumin dai ya haiƙe wa tsohuwar ne bayan ya labbace ta. 

Mai magana da yawun ƴansandan ya ce,

“An zarge shi da shiga gidan tsohuwar mai shekara 80, wacce take zaune ita kaɗai a gidan, sanna ya yi mata fyade"

Ya ƙara da cewa,

“Bayan mun samu wannan labarin, ƴansandan da ke ofishinmu na Garaku sun ɗauki mataki nan take inda suka kama mutumin da ake zargi."

Kwamishina ƴansandan Jihar, CP Adesina Soyemi, ya bayar da umarni a kai batun sashen binciken masu aikata manyan laifuka da ke Lafia domin gudanar da bincike a kan mutumin da ake zargi.

Wasu Labarai:

  1. Dattawan Arewa Sun Ce Shugaba Buhari Ya Basu Kunya
  2. Yadda Yan Wasan Najeriya Suka Lallasa Masar da Sudan
  3. Matasa Sune Jigon Siyasa a Kowace Tafiya

Post a Comment

0 Comments