Daga: Muhammad Abdallah
ZAMFARA, NAJERIYA - 'Yansandan a Jihar Zamfara sun kama wasu mutane da
ake zargi da sayar da sassan jikin mutum. Wannan wani al’amari ne da ya
tsoratar da mutane ya kuma saka shakku a zukatansu musamman a Jihar ta Zamfara
da ba a saba ganin irin wannan ba Jihar tafi fama da hare-haren ɓarayin daji. A
ranar alhamis ne a taron manema labarai da ya gudana, Kwamishinan 'yansanda
Ayuba Elkana sanar da cewa,
“An damke waɗansu mutum huɗu da
ake zargi ne bayan da jami'an tsaro suka tsinci gawa a wani kango, ba tare da
wasu sassan jikinta ba”.
Kwamishinan ya yi ƙarin bayani
inda ya ce, an fara binciken gano wani yaro ne daya ɓara, sai aka wata gawa a
wani kango kuma babu wasu sassan jikin gawar. Bayan an faɗaɗa bincike sai aka
kama wasu mutum huɗu magidanta biyu sai matasa biyu waɗanda ake zargi da kashe
wannan gawa. Wannan ne yasa aka ƙara faɗaɗa bincike kuma yanzu haka ana
binciken wasu ƙungiyoyi da ake zargi na ci da sayar da naman mutum a cikin
Jihar.
Bisa wannan bincike da ake yi an
gano cewa, shugaban wata ƙungiya da ake zargi ya tura kuɗi har naira ɗubu ɗari
biyar ga ɗaya daga cikin mutanen da aka kama, kuma ana zargin cewa kuɗin na
cinikin sassan jiki ne da suka yi.
Jihar Zamfara na ɗaya daga cikin
jahohin dake fama da hare-haren ɓarayin daji masu satar mutane don karɓar kuɗin
fansa, amma ba a saba jin labarin ci ko sayar da naman mutum a cikin jihar ba,
sai a wannan karo da aka kama mutum huɗu waɗanda ake zargi. Ko a satin daya
gabata jami’an ‘yansanda sun kuɓutar da wasu mutane da aka sace, haka kuma an
sake kuɓutar da wasu da aka ɗauke da Jihar Kaduna tsakanin Kaduna da Birnin
Gwari.
A ɗan tsakanin nan an kashe fiye
da mutane ɗari biyu a cikin Jihar kawai, inda aka kashe wasu daruruwa a faɗin ƙasar
baki ɗaya. Kodayake ɓarayin dake addabar Jihar sun yi yunƙurin neman sasanci
inda har wani shugaba daga cikin shugabanin ɓarayin dajin wanda aka fi sani da
suna Bello Turji ya sako wasu ɗimbin mutane da ƙoƙarinsa na ya samu ayi sasanci
tsakaninsa da gwamnati.
Jihohin Katsina da Kaduna da
Zamfara da Sokoto da Kebbi na fama da hare-haren ɓarayi masu satar mutane don
karɓar kuɗin fansa.
Wasu Labarai:
- An Kama Wata Mata Zata Saida Ɗan Kishiyarta A Zamfara
- Sojoji Sun Kuɓutar da wasu Matafiya
- Wani Bawan allah ya Roƙi QS Yakubu Manni Ya fito Takara
0 Comments