Talla

An Dasa Zuciyar Alade ga Wani Mutum Ɗan Shekara 57

 #Arewanews

Daga: Hauwa'u Bello

11 Janairu, 2022

ABUJA, NAJERIYA - Likitoci a Jami’ar Maryland ata Koyon Kiniyar Maɗa Magunguna wato (UMSOM) sun yi nasarar dasa zuciyar alade da aka sauyawa kwayoyin halitta sannan aka dasa wa wani mutum mai shekaru 57 da ke da cutar zuciya mai suna David Bennett.

An bayyana haka a cikin wata sanarwa da cibiyar ta fitar inda ta bayyana cewa, an gudanar da aikin tiyatar mai cike da tarihi a ranar Juma’a.

Sanarwar ta ce, 

Bennett yana kwance a asibiti na tsawon watanni kuma an haɗa shi da na’uroro don ci gaba da rayuwa gabannin fara aikin.

Dashen zuciyar ta alade shi ne zaɓi ɗaya tilo ga mara lafiyar da aka ce yana fama da cutar arrhythmia mai barazana ga rayuwarsa.

Cibiyar ta ce, ba za a iya yi wa mutumin dashen zuciya na yau da kullun ba kamar yadda Cibiyar Kiwon Lafiya ta Jami’ar Maryland (UMMC) da sauran manyan cibiyoyin dashen da suka yi bitar bayanan lafiyar mutumin.

Mutumin ya ce,

“Ina so in rayu, amma zaɓina ne na ƙarshe shi ne ayi mani wannan dashe. Ina fatan tashi daga kan gado bayan na warke.” 

Hukumar dake Amurka ta ba da izinin gaggawa don yin tiyata a ranar 31 ga Disamba, shekara ta 2021 don a samu a ceto marar lafiyar.

Babban likitan da ya jagoranci tiyatar ya ce,

 “Nasarar tiyatar ta kawo mana mataki ɗaya na magance matsalar karancin zuciyoyi.”

Ya ƙara da cewa,

“Muna ci gaba da taka-tsantsan, amma kuma muna da kwarin gwiwar cewa wannan tiyata ta farko a duniya za ta samar da wani muhimmin sabon zabi ga marasa lafiya a nan gaba.”

A nasa ɓangaren, Muhammad Mohiuddin, farfesa a fannin tiyata a UMSOM wanda ya kafa shirin xenotransplantation na zuciya tare da Griffith, 

"Ya ce tsarin zai ba da fa’ida don magance cututtukan zuciya".

Za a sanya ido kan Bennett a cikin makonni masu zuwa don tantancewa ko dashen ya samar da fa’idar ceton rai.

Likitocin marar lafiyar sun kuma ce za a iya cire shi daga na’urar a ranar Talata, tun bayan sa’o’i 48 na farko, waɗanda aka ce suna da matuƙar muhimmanci su wuce ba tare da wata matsala ba.

Wasu Rahotanni

  1. Khalifan Tijjani Sarki Muhammadu Sanusi Lamiɗo II Ya Ja Kunnen Mutane da cewa Kar su Bi Jam'iyya ko Addi a Zaɓɓukan 2023
  2. Rundunar Sojojin Najeriya ta Gargaɗi Sheikh Ahmed Gumi
  3. Osinbajo Ya Tafi Ghana Don Wakiltar Shugaba Buhari A Taron Ecowa

Post a Comment

0 Comments