1 Janairu, 2022
ZAMFARA, NIJERIYA - Rundunar ƴansandan NIjeriya dake Jihar Zamfara ta ceto ƙananan yara guda ashirin da ɗaya 21 waɗanda aka yi garkuwa da su, cikin yaran akwai mata guda biyu. An sace yaran ne a hanyarsu da zuwa makarantar almajirici dake Jihar Katsina.
Mai magana da yawun Rungunar ƴansanda ta Jihar Zamfara wato SP Mohammed Shehu ya ce, yaran sun taso ne daga ƙauyen Rini da ke Ƙaramar Hukumar Bakura ta Jihar Zamfara za su tafi makaranta dake Jihar Katsina.
Jami'an tsaron sun samu labarin cewa ƴan bindiga sun tare hanyar Gusau zuwa Funtua ta ɓangaren Kucheri, bayan sun tare hanyar ne suka sace yaran tare da yin garkuwa da wasu mutanen waɗabda ba a san adadinsu.
Jami'ai sun isa wurin da abun ya faru inda suka yi musayar wuta da ƴan bindigan.
Ƴansandan Zamfaran dai sun yi kira ga direbobi da fasinjoji da su kiyayi tafiyar dare inda suka ce akasari da dare ne ɓarayi ke tare hanya.
Garuruwan Katsina da Kaduna da Zamfara da Sokoto da Kebbi na fama da hare-haren ɓarayin daji masu satar mutane don karɓar kuɗin fansa.
0 Comments