08 Janairu, 2022
Daga: Muhammad Abdallah
ZAMFARA, NIJERIYA - An
binne gawarwakin mutume 143 waɗanda ɓarayin daji suka kashe, an kashe mutanen
ne a wani hari da ƴan bindiga suka kai a ranar Laraba da kuma ranar Alhamis a
ƙauyuka dake ƙarƙashin Ƙananan Hukumomin Anka da Bukuyyum da ke Jihar Zamfara. Bayan
waɗannan gawarwaki, akwai wasu da ɓarayin suka kashe suka kuma daddatsa gangar
jikinsu sannan kuma suka ƙona gawarwakin wasu ƙurmus.
Wani ganau ya shaida cewa akwai abubuwan ban tsoro da tashin hankali
da ɓarayin suka aikata, bayan sun kashe mutane, sun kuma cinna wa wasu gidaje
wuta inda wasu iyalai ke ciki, iyalan mata da yara da magidanta duk sun ƙone
kurmus.
Rundunar sojojin Nijeriya ta tura jirgin yaƙi domin fatattakar ɓarayin
dajin amma jirgin bai taɓuka komai ba, saboda ɓarayin sun yi dubara sun shige
sun ɓoye cikin mutanen gari. Ɓarayin
bindiga dai suna ƙara matsawa cikin dazuzzuka saboda matsawa da sojoji suke
masu, haka kuma suna faɗaɗa hare-harensu duk a yake dai wasu daga cikin
sanannun ɓarayin suna ta ƙoƙarin ayi masu sasanci.
Ko satin daya gabata, wannan shahararren ɓarawon wanda aka fi sani
da sunan Bello Turji ya sako duk mutanen da ya sace don karɓar kuɗin fansa. A niyarsa
ta yin sasanci da gwamnati. Ƙauyuka da garuruwa da dama a Jihar Zamfara na
fuskantar barazana da hare-hare daga ƴan bindiga. Gwamnati ta bayyana cewa an
tura jami'an tsaro domin yaƙar waɗannan ɓarayin dajin.
Garuruwan Katsina da Kaduna da Zamfara da Sokoto da Kebbi na fama da
hare-haren ɓarayi masu satar mutane don karɓar kuɗin fansa, kodayake Sojojin ƙasar
na bakin ƙoƙarinsu wajen daƙile hare-haren ɓarayin.
0 Comments