02 Janairu,2022
KATSINA, NIJERIYA - Wasu ɓarayin daji sun sace matafiya da yawa da ke bisa hanyarsu ta zuwa Jihar Zamfara waɗanda suka fito daga Jihar Katsina.
Ranar Juma'a da daddare da kuma safiyar Asabar ɓarayin dajin sun kai hari kan motocin fasinja kusan goma, sun kwashi mutane da dama tare da kashe wasu.
Wata mata da ke cikin wata mota ta faɗi yadda lamarin ya faru. Ta ce,
Sun taso daga Jihar Katsina inda suka nufi Jihar Zamfara. Suna cikin tafiya da misalin karfe huɗu na yamma sun isa Funtua da misalin ƙarfe bakwai da wani abu. Daga nan suka wucd garin 'Yankara zuwa garin Kuceri. Sai suka ji ƙarar harbi ta ko ina.
Ta ci gaba da cewa, bayan direban motar ya ji harbe-harbe sai ya juya motar zuwa cikin gona, inda ya koma kan titi, amma sai ɓarayin suka harbi tayar motar guda ta baya.
Ta ce saboda harbin, gilashin motar ya watse kuma ya ji mata ciwo, haka kuma sun harbi wata mata a gefen kanwa wanda ya yi sanadiyar rasa ranta. Daga nan ne direban motar ya wuce da su zuwa garin Wanzamai inda ya nemi taimako.
Ba wannan motar kaɗai aka tare ba, akwai wasu motoci da tireloli da aka tare. inda aka ɗauki mutane da dama aka kuma kashe wasu.
Ko a shekaranjiya ranar juma'a saida wasu ɓarayi suka tare hanyar Katsina zuwa Jibiya, amma basu daɗe ba suka tashi kuma ba su ɗauki kowa ba.
Amma wani ganau ya shaida wa Arewa News cewa, ya ga ɓarayin da idonsa, a daidai inda ake kira da Mil takwas ɓarayin dajin suka fito daga dajin ƙauyen Daga, bayan sun hau babbar hanya suka yi harbe-harbe sannan suka shige dajin Bugaje. Ganau ɗin ya fada mana cewa, ɓarayin da ya gani za su kai mashin arba'in kowane mashin na ɗauke da mutum uku. Daidai lokacin da suka hau babbar hanya sai mutane biyu dake saman kowane mashin suka miƙe tsaye sannan suka buɗe wuta da bindigoginsu.
Garuruwan Katsina da Kaduna da Zamfara da Sokoto da Kebbi na fama da hare-haren ɓarayin daji masu satar mutane don karɓar kuɗin fansa.
0 Comments