Daga: Bello Hamisu
07 Janairu, 2022
Allah Ya yi wa babban malamin addinin nan na Kano Sheikh Ahmad Muhammad Ibrahim Bamba, wanda aka fi sani da 'Ƙala Haddasana' rasuwa a yau Juma'a.
Fitaccen malamin ya yi fice ne a wajen karatuttukan Hadisai da ma wasu litattafai. A can baya kafin ya buɗe tashi makarantar ya yi karatuttukansa a Masallacin BUK wanda a nan ne ma ya samo sunan 'BUK'.
Malamin ya rasu bayan ya yi fama da gajeruwar rashin lafiya har ya kwana ɗaya a Asibitin Koyarwa na Malam Aminu Kano.
Iyalansa sun sanar da cewa za a yi jana'izar malamin a Masallacin Darul Hadis da ke unguwar Tudun Yola a birnin Kano bayan Sallar Juma'a.
Malamin zai yi shekara 82, iyalansa sun ce an haife shi a shekarar 1940. An haifi Malamin a ƙasae gana, daga baya ya dawo Nijeriya da zama. Ya yi karatun Digirinsa a Saudiyya sannan ya fara koyarwa a Jami'ar Bayero ta Kano kuma a nan ne ya yi digirin-digirgir.
Ya yi koyarwa a fanin Nazarin Ilimin Musulumci. Malamin ya bar yara da matansa. Allah ya jiƙansa da rahma. Ya kyautata macinsa yasa mu iske su cikin amincin Allah muna amintattun bayinsa.
0 Comments