Labarin Buba Da Aljannar Ruwa
Daga: Littafin Hikimarka Jarinka na Bello Hamisu Ida
A zamanin da an yi wani mashahurin matashin mashayin giya, mai suna Buba,
a garin Argungu ta ƙasar Kebbi. Duk yankin
ba wanda ya iya ɗaga ƙoƙon burkutu kamar Buba.
Wai har gasar ɗaga ƙoƙon burkutu ake yi da shi. In ya fara kwankwaɗar
barasa sai ya yi sati biyu a mashaya. Ya kan yi fiye da kwana uku yana sharar
barci. Wannan ta sa mutane suka tsane sa duk inda ya je sai hantara da kyara,
babu inda yake shan ruwa sai a mashaya. Babbar sana’arsa ita ce Su.
Buba yana samu sosai da wannan sana’ar tasa amma mashaya ba ta barin
sa adana komai. Har ta kai da dare yake fita Su, ya kamo kifi ya dawo da safe
ya sayar da abin da ya kamo, ya tafi mashaya sai wani dare.
Wata rana wasu ‘yan su mutum huɗu suka shiga kwale-kwale sai ruwan
Argungu don su yi kamun kifi, ciki kuwa har da Buba, suka wurga tarunsu don
neman sa’a. Shi kuwa Buba sai ya fanjama cikin ruwa yana ta lalube yana neman
sa’a, ya yi iyo can sai ya cafko hannu, ya jawo ya yi sama yana fitowa ya jawo
wannan hannu zuwa bakin ruwa, a zatonsa wani ɗan uwansa ne ya yi gajen rai, ga
mamakinsa sai ya jawo wata samɓaleliyar budurwa mai kyau, ta ci ado ta sa kambu
irin na Sarauniya a sume, Buba ya jira ta farfaɗo sannan ya ce,
“Baiwar Allah daga ina haka?”
“Ni ba mutum ta ba, aljana ta,
shawagi na fito wani mutum ya kammin da wasu ƙarahuna (fatsa) amma sai ka
cetomin raina, don haka zanyi maka abin alƙairi.”
Ta amsa cikin sassanyar murya.
Tana gama faɗar haka sai ta rikiɗe rabin jikinta ya koma kifi rabi
kuwa na wannan kyakyawar Sarauniya, ta yi cikin ruwa, Buba ya zauna yana Mamaki
gashi nesa da mutane.
Yana nan kafin ya tashi sai wasu kifaye suka yunƙuro cikin ruwa suka
ja ƙafafuwansa suka yi cikin ruwa da shi. Suka ci gaba da tafiya da shi har faɗar
Sarauniyar Aljannun ruwa. Ga kilisai nan kala-kala da kujeru masu ban sha’awa,
Buba ya zauna bisa wani lallausan kilishi, dabbobin ruwa sai kawo caffa suke yi
wajen Sarauniya.
Sarauniyar Aljannu ta yi wa Buba kyautar taskar zinariya, ta ce
masa,
“Ka tahi duk bayan wata shidda, ka zaka ka ɗibi kaso daga cikin
zinaran ga. Amma kam da sharaɗi, kada ka taho in ba bayan wata shiddan da nac ce
ma ba, kuma kada ka taho da wani. Inko hakan ya faru, duk abin da nib ba ka ɓacewa za su yi.”
Ta kawo laya ta ba shi duk lokacin
da yake son zuwa fadarta ya zo bakin ruwan ya murza ta, kifaye za su fito su yi
masa jagora zuwa fadar Sarauniyar ruwa.
Buba ya yi godiya ya ɗebi dukiya aka fitar da shi, ya koma Birnin Kebbi da zama. Nan fa Buba ya shiga barazana da dukiya, da facaka da kuɗi, ya shiga bushasha. Kullum sai ya tara makiɗa da mawaƙa a ƙofar gidansa, a yi rawa a sha barasa a watse. Haka mutane ‘yan abi yarima a sha kiɗa suka rinƙa kawo wa Buba caffa, suna ɗibar rabonsu.
Wata shidda
ba ta yi ba dukiyar ta ƙare. Ya kwashi jiki ya koma wajen Sarauniyar Aljannu ya
gaya mata cewa, wani bala’i ne ya faɗawa wa dukiyarsa. Ta sake ba shi wata amma
ta gargaɗe shi kar ya sake dawowa, in kuwa ya dawo ya karya doka.
Buba ya koma ya ci gaba da bushasha. Rannan ya sha ruwan barasa ya ƙoshi,
ya tara ɓarayi majiya ƙarfi, ya gaya masu su shirya gobe za su je cikin ruwan Argungu
su yi sata a gidan sarauniyar ruwa!
Tun da Asubahi ɓarayin da suka samu labarin zuwa gidan sarauniyar
ruwa, suka ɗunguma sai ruwan Argungu, suka fantsama cikin ruwa suka far wa
kifayen da ke cikin ruwan Argungu, suka yi ta kama su. Gurinsu su kama wanda
zai kai su wajen da dukiyar sarauniyar ruwa take, don su kwashi rabonsu.
Sarauniya tana fada ana ta faɗanci, sai ga wasu bayinta daga cikin
kifaye, suka gaya mata abin da ke faruwa, cewa ɓarayi sun far masu da kamu suna
ta kisansu, ta umurci mutanenta su tashi daga wannan ɗaula. Aka yi shela,
Sarauniya ruwa da mutanenta suka tattara kayansu suka bar Argungu.
Wasu Labarai
- Labarin Jatau Mawaƙi
- Labarin Akuya mai Magana
- Labarin Ƙaiƙayi Koma Kan Masheƙiya
- Labarin Na Shiga Ban Ɗauka Ba
- Labarin Sarkin Dawa
- Labarin Aikata Alheri Duk Inda Ka ke
- Labarin Ka So Naka, Duniya Taƙi Sa
- Labarin Ɓarawon Birni Da na Ƙauye
Buba ya ruɗe ya haukace ya rinƙa bin gari yana faɗar irin dukiyar
dake Daular Sarauniyar ruwa. Su kuwa mutanen gari da suka samu labarin dukiyar
dake cikin Dam ɗin Argungu sai su ka ci gaba da kama kifiyen waɗanda ba su yi ƙaura
da Sarauniyar ruwa ba. An ce wannan shi ne asalin kafa gasar kamun kifi a Argungu.
Yanzu haka in ƙarshen shekara ta zagayo za ka ga ‘yan su a Dam ɗin Argungu suna
ta gasar kamun kifi.
Tun daga wannan lokacin duk dukiyar da yake taƙama da ita ta ɓace,
mutane suka guje shi, dama don dukiyarsa suke tare da shi. Buba ya sha komawa
wajen Sarauniya don ya yi mata wata ƙarya, ya kasa samun hanyar shiga ruwan,
layar da ta ba shi ta ɓace. Talauci ya dawo sabo, har hauka ya kama shi. Duk
inda ya wuce sai ka ji yana cewa,
“Saurauniyar ruwa, Sarauniyar Aljannun ruwa”.
0 Comments