Talla

Abin da nake Dubawa Kafin in Yarda a Sumbace ni a Fina-finai — Queeneth Agbor

 Daga: Hauwa’u Bello

ABUJA, NAJERIYA — Yin sumbata wani baƙon al’amari ne a cikin fina-finanmu na Hausawa, wanda ya saɓawa addininmu da al’adarmu kuma kai tsaye nuna shi yana taimakawa sosai wajen taɓarɓarewar tarbiyya. Kodayake ga wasu ƙabilu babu haramci yinsa, don haka a kan nuna shi a cikin wasu fina-finai na kuɗancin ƙasar Najeriya da ma wasu fina-finai na wajen Najeriya musamman fina-finan Turawa da Indiyawa. Tauraruwa Quenneth Agbor ta taɓa bayyana takaicita a kan yadda wasu taurari ke aikata masha'a a bainar jama'a.

Quenneth Agbor shahararriyar turaruwa ce dake fitowa a fina-finan kudancin Najeriya, ta faɗi wasu dokoki da ta sanya kafin ta sumbaci wani tauraro a cikin fim.

An yi firar da Quenneth Agbor Kehinde Ajose a ranar 15 ga watan Janairu shekara ta 2022 Jaruma, Ƙueeneth Agbor ta ce,

Kafin ta amince da wani don su yi sumbata a cikin fim, sai ta kula da wasu abubuwa.  Ta ce,

“Duk ɗan wasan da zan amince in sumbata, sai ya zama yana fitar da numfashi daga bakinsa mai kyau”

Wato yana yin numfashi mai ƙamshi, ba wai mai fitar da wani abu daban ba. Ta ƙara da cewa,

“Samun numfashi mai kyau yana da mahimmanci a gare ni kuma fitar da iska mai ƙamshi ta baki yana da mahimmanci sosai wajen yin sumbata. "

Da aka tambaye ta ko ta taɓa samun mummunar sumbata a lokacin da take ɗaukar fim, sai ta ce,

“Wani ɗan wasa mai warin baki ya so ya sumbace ni, amma sai na ƙi yarda, ko lokacin da ya kawo bakinsa kusa ni, sai na ji wani irin numfashi da iska marar daɗi na fita, sai na janye bakina daga gare shi"

Ta ƙara da cewa,

“Dole Daraktan fim ɗin ya dakatar da shirin don ya fahimci abinda na ji”

Duk sumbatar da taurarin ke yi suna ɗaukarshi a matsayin wasa ne. Wasu daga cikin dokokin da take bi kafin ta yi sumbata sun haɗa da, bata son namiji mai ƙazanta mai fitar da tsamin jiki ko tsamin baki, haka kuma bata son namiji wanda baya gyara gashin jikinsa, kuma bata son namiji marar tsaftar haƙora.

Jarumar ta bayyana takaicinta na yadda wasu taurari ke yawan yin faɗa a shafukan sada zumunta, ta ce,

“Na ɗauke shi wauta ace mutum mai mutumci ya tsaya yana faɗa a dandalin sada zumunta”

Ta ƙara da cewa,

“Lokacin da ake faɗa a dandalin sada zumunta, wasu za su so su saka ido sannan su buɗe kunnuwansu don su ji abinda ake faɗa kanshi, bayan an gama faɗan kuma zaka ji maganganu maras sa daɗi game da abinda ya faru”

Da aka tambayi jarumar game da sabuwar shekara, sai ta kada baki ta ce,

 “Ban shiga cikin wannan sabuwar shekara da guruka masu yawa ba, abinda kawai nake mayar da hankali a gare ni shi ne, yadda zan faɗaɗa kasuwanci na a cikin wannan shekara in kuma samu ƙarin kuɗi”

Ta ƙara da cewa,

“Ba ni da halaye maras sa kyau, don haka bani da gurin ƙuntatawa wani a cikin shekarar 2022."

Wasu Labarai:

  1. 'Yan Bindiga Suna Yin Shigar Mata Don Kai Hari A Yankunan Sokoto
  2. An Kama Masu Ci da Saida Naman Mutum
  3. An Kama Wata Mata Zata Saida Ɗan Kishiyarta A Zamfara

Post a Comment

0 Comments