#Arewanews
Daga: Muhammad Abdallah
11 Janairu, 2022
KANO, NIJERIYA - Rundunar
'yan sandan Najeriya dake Jihar Kano ta kama wani matashi wanda ke zaune a
Ƙaramar Hukumar Tofa da bisa zargin yin garkuwa da wata yarinya wadda aka sani
da suna Zuwaira Gambo, yar shekara 13, wadda aka fi sani da sunan Siyama, bayan
ya yi garkuwa da ita sai ya yi mata yankan rago.
Rundunar 'yan sandan ta ce, ta samu gawar
Zuwaira a wani kango da ke garin Tofa, bayan kwana ɗaya da ɓatan ta. Taga baya
ne rundunar ta kama matashin bayan an daɗe ga binne gawar yarinyar.
DSP
Abdaullahi Haruna Kiyawa a shafinsa na Fesbuk ya yi ƙarin bayanin yadda abun ya
faru, ya ce matashin mai suna Auwalu Abdulrashid ɗan shekara 21 wanda ake wa laƙabi
da lauje yana zaune kusa da gidansu yarinyar.
Lauje ya yaudari yarinyar ya ce zai sayi
fanke sannan ya sace ta, bayan matashin ya sace yarinyar sai ya kira iyayenta
inda aka fara ciniki, ya kuma nemi miliyan ɗaya a matsayin kuɗin fansa, ciniki
ya faɗa a kan cewa za a bashi naira dubu ɗari huɗu, amma kafin a kai masa kuɗin
sai aka tsinci gawar yarinyar.
Mahaifin Zuwaira ya shaida cewa, ya tsinci
gawar ɗiyarsa a daidai lokacin da yake ƙoƙarin kai kuɗin fansa. Kafin ya kai kuɗin
sai kuma ya samu wani mumunan labari cewa an kashe ta, ya samu gawarta an rufe
mata baki sannan daga bisani aka yi mata yankan rago.
DSP Abdullahi Kiyawa ya ƙara da cewa,
"Lauje ya yaudare ta, ya kai ta kango,
sannan kuma ya ɗauki hijabinta ya shaƙe mata wuya ya ɗauko wuƙarsa ya yanka ta
saboda ta gane shi."
Ya kuma ce,
“Daga nan ne wanda ake zargin ya ɗauki
fatanyarsa ya haƙa rami sannan ya binne ta a wani kango da ke kusa da gidansu”.
Bayan kashe Zuwaira da daɗewa, sai kuma wanda
ake zargi ya sake sace ƙanin Zuwaira wato Muttaƙa ɗan shekara uku sannan ya
nemi kuɗin fansa har naira miliyan biyu.
Bayan an yi ciniki sai aka daidaita za a bashi naira dubu ɗari, aka
bashi kuɗi sannan ya sako yaron. Daga bisani dai aka kama yaron.
Ba kasafai ɓarayin
daji suka cika yin ta’asa a Jihar Kano ba, amma kwanaki kaɗan da suka wuce wasu
ɓarayi suka yi garkuwa da mahaifiyar wani ɗan majalisa dake jihar Kano.
Jihohin Katsina da Zamfara da Sokoto da Kebbi
da Kaduna na fama da hare-haren ɓarayin daji masu satar mutane don karɓar kuɗin
fansa.
Wasu Labarai:
- An Kaddamar da Kungiyar Neman Zaben Mustapha Inuwa A Danja
- Yan Bindiga Sun Sace Mahaifiyar Danmajalisa a Kano
- Masari Ya Canza Zaɓen Ƙananan Hukumomi
0 Comments