Talla

'Yar Kano ta lashe Gasar Sarauniyar Kyau ta Nijeriya

Daga: Hauwa'u Bello Jihar Kano
18 Disamba, 2021

KANO, NIJERIYA - Shatu Garba wadda aka haifa a garin Kano dake Arewacin Nijeriya ita ce ta lashe Gasar Sarauniyar kyau ta ƙasar.

Yarinyar ƴar shekara 18, ta sha gaban wasu matan 18 a bikin da aka gudanar a ranar Juma'a da daddare a Landmark Centre da ke birnin Legas.

Wani abun birgewa, Shatu ita ce mace ta farko da ta sanya hijabi a wajen gasar ta kuma lashe gasar, wannan ba ƙaramin tarihi bane, wannan ne karo na arba'in da huɗu da aka yi gasar wadda ake kira Miss Nigeria.

Wata yarinya mai suna Nicole Ikot ce ta zo ta biyu, sai kuma Kasarachi Okoro da ta zo ta uku.

Shatu Garba Ta karɓe kambun ne daga hannun Etsanyi Tukura 'yar Jihar Taraba, wadda ta lashe gasar a karo na 43 a shekarar 2019.

Masu shirya gasar sun ce, wadda ta zo ta ɗaya za ta samu kyautar kuɗi naira miliyan 10, da zama a gidan alfarma na shekara ɗaya, da sabuwar mota, da kuma zama jakadiya ga wasu kamfanoni.

An samu sauye-sauye a cikin gasar tun daga yanayin kwalliyar masu shiga gasar da suturarsu da kuma karɓuwar su ga al'umma. 

Shatu Garba wato Sarauniyar Kyau ta Nijeriya ta 44, ƴar asalin Jihar Kano ce kuma ita ce ta wakilci yankin Arewa maso Yammacin ƙasar. Ƴar shekara sha takwas ɗin tana tallar hijabai kuma tana sha'awar hawa doki. An sha ganin hotunanta tana bisa doki inda wasu lokuttan take tallata hijabai.

Post a Comment

0 Comments