Talla

Yan Bindiga Sun Sace Basarake a Jihar Filato

Daga: Hauwa'u Bello
26 Satumba, 2021

ABUJA, NIJERIYA - 'Yan bindiga sun ɗauke wani basarake mai suna Charles Mato Daka, Basarake ne a garin Gindiri a Jihar Filato, rahoton da ya fito daga Daily Trust ne ya faɗi haka.

Ta ruwaito cewa an ɗauke Sarkin ne har gidansa da ke Ƙaramar Hukumar Mangu bayan ɓarayin sun yi ta harbi kan mai tsautsayi da asubahin yau Lahadi.

Mai magana da yawun rundunar Operation Safe Haven ta sojojin Najeriya a Filato wato Manjo Ishaku Takwa, ya tabbatar da faruwar wannan al'amari.

Ya ƙara da cewa, an tura jami'an tsaro zuwa wajen da lamarin ya faru domin bin diddiƙi abin da ya faru.

Ko a ranar Asabar ƙungiyar ƙabilar Igbo ta Ohanaeze Ndigbo da kuma Afenifere ta Yarabawa sun bayyana takaicinsu kan yadda ƴan bindiga a Arewacin Nijeriya ke kashe mutane.

Garuruwan Katsina da Kaduna da Zamfara da Sokoto suna fama da sace-sacen mutane don karɓar kuɗin fansa.

Post a Comment

0 Comments