Talla

Yadda ake tace Man Fetur wato Crude oil a Turance

Disemba 16, 2021



ABUJA, NIJERIYA — Man Fetur, wanda kuma aka fi sani da ɗanyen mai ko crude oil a turance, ruwa ne mai tasowa, yana da launin rawaya da baƙi amma baƙin yafi cizawa sosai, ana samun sa a cikin ƙarƙashin ƙasa ko teku ko ƙarƙashin duwatsu. Yawanci ana tace man fetur a fitar da nau'ikan mai da dama tun daga kalanzir da fetur da gas da sinadarin da ake roba da sinadarin kwalta da kuma sinadarin man shafawa da sauransu.

Ana raba nau’ikan man fetur ta hanyar amfani da wata fasaha mai suna fractional distillation a turance, wato cakuɗa ruwa don a fidda wasu nau’ika zuwa ɓangarori da dama, ana amfani da ginshiƙi mai raguwa wajen tabbatar da fasahar tace mai. Man fetur ya ƙunshi sinadarin hydrocarbons da nau'ikan kwayoyin halitta daban-daban haka kuma akwai kwayoyin halitta iri-iri a cikinsa.

Sunan man fetur ya haɗa da duka ɗanyen mai da ba a sarrafa su a zahiri da kuma kayayyakin man fetur wadanda suka haɗa da tataccen mai. Man fetur yana samuwa ne lokacin da matattun halittu masu yawa, akasari ‘yan ƙanana ne dake rayuwa a cikin ruwa ana kiransu da zooplankton ko algae a turance, ko hallitun da suka mutu aka binne su a ƙarƙashin dutse, sannan aka fuskanci zafi mai yawa sai waɗannan matattun hallitu su rikiɗe su zama kwayoyin man fetur.

An fi samun man fetur ne ta hanyar hako mai. Ana gudanar da hakowa ne bayan nazarin ilimin yanayin ƙasa, da ilimin yanayin tafki. Da zarar an hako mai, sai a tace mai kuma a raba shi, akan fitar da ruwan man fetur, dizal da kananzir da kwalta da sinadarai da ake amfani da su wajen kera robobi, magungunan kashe ƙwari da sauransu.

An kiyasta cewa duniya tana cin ganga miliyan 100 a kowace rana. Ƙasashe da dama sun dogara da man fetur saboda buƙatuwarsa da kuma yawan amfani da shi, ana samun riba da bunƙasa tattalin arziƙi, wasu ƙasashe sun samu ƙarfin tattalin arziki saboda yadda suke sarrafa albarkatun man.

Wajen hakar man fetur, da tacewa da kona man fetur a kan fitar da iskar gas mai yawa, don haka man fetur yana daya daga cikin manyan abubuwan da ke taimakawa wajen sauyin yanayi. Bayan wannan akwai wasu illoli da hakar man fetur ke haifarwa ga muhalli, misali kamar malalar mai da gurɓacewar iska da ruwa da wuraren zama. Bayan wannan, man fetur ya kasance tushen rikice-rikicen da ke haifar da yaƙe-yaƙe na ƙasa da sauran nau'o'in rikice-rikice.

 

 

Post a Comment

0 Comments