Daga: Hauwa’u Bello
27 Disamba, 2021
KADUNA,
NIJERIYA — Wasu
mafarauta dake kauyen Udawa a ƙaramar hukumar Chikun a Jihar Kaduna dake
Arewacin Nijeriya sun kama wani ɗan bindiga a wani daji da ke kan hanyar Kaduna
zuwa Birnin Gwari.
Mafarautan
sun kuɓutar da wasu mutum tara a ƙauyen waɗanda aka yi garkuwa da su a farmakin
da suka kai wa ɓarayin dajin.
Jaridar
Aminiya ta rawaito cewa mafarautan sun yi wa ɓarayin kwanton bauna bayan da
suka far wa ayarin motocin matafiya a kan babbar hanyar.
Jihohin
Katsina da Kaduna da Zamfara da Sokoto da Kebbi na fama da hare-haren ɓarayin
daji masu satar mutane don karɓar kuɗin fansa.
0 Comments