Daga: Aminu Abdullahi Mohd
Ga ta nan, ga ta nanku.
Wata rana wasu 'yan matan ƙauye suka
tafi rafi su, wato kamun kifi. Suka kuma yi sa'a suka kamo kifaye, suka kama
hanya suka koma gida. A kan hanyarsu ta zuwa gida sai suka haɗu da wata tsohuwa
sai ta tsayar da su, ta roƙi su sam mata kifin da suka kamo, ko da mai ƙaya ne.
Sai suka hana ta. Amma sai wata budurwa daga cikinsu ta ɗeba mata kifin ta bata. Tsohuwa ya karɓa,
ta gode mata suka tafi.
Washe-gari da suka koma rafi don
kamun kifin mai yawa, ƙoransu cike maƙil. Da tsohuwar nan ta roƙe su, suka hana
ta sai waccan budurwa da ta bai wa tsohuwa kifin jiya ta gaya mata cewa yau ba
ta samu ba sai wasu 'yan ƙanana guda biyu kawai. Ga shi kuma tana jin tausayin
'yar tsohuwar. Saboda haka sai ta ba ta ɗaya, ita kuma ta riƙe ɗaya. Kafin su
rabu, sai tsohuwar ta gaya mata in ta je gida da wannan kifi guda ɗaya da ya
rage a hannunta, kada ta dafa shi ta sanya shi a cikin randar gidansu. Bayan ta
isa gida sai ta saka kifin a cikin randar kamar yadda tsohuwa ta ce ta yi. Sai
ta shiga ɗaki ta kwanta. Da gari ya waye sai ta buɗe randa don ta ɗauki ɗan
kifinta, amma sai ta ga randa ta cika maƙil da manya-manyan kifaye. Ta yi ta ɗiba,
amma kifayen nan ba sa ƙarewa.
Bayan 'yan kwanaki 'yan mata suka koma rafi don su kamo kifi, amma wannan ranar ba su samu komai ba, sai suka koma gida babu kifi.
Washe-gari sai aka yi shela a gari cewa Sarki yana son ya
ci kifi, kuma duk budurwar da ta kamo kifi ta dafa wa Sarki ta kai masa zai
aure ta. Gaba ɗayan 'yan matan ƙauyen suka fita kamun kifi, amma ba wadda ta
samo sai wannan budurwa da takan ba tsohuwa kifi.
Yadda aka yi ta samo kifin nan kuwa shi ne, da ta kama hanyar rafi sai ta haɗu da wannan tsohuwar. Sai tsohuwa ta ce mata kada ta je babban rafi, ta nuna mata wata hanya da za ta kai ta har bakin wani ƙaramin gulbi.
Sai tsohuwa ta ce ta yashe ruwan. Da budurwa Marainiya ta fara yashewa sai ta fara ganin manyan kifaye, ta yi ta ɗiba har ƙwaryarta ta cika, ta koma gida.
A duk faɗin garin budurwar nan kaɗai ce ta kamo kifi a
wannan rana. Bayan ta dafa kifi ta sa a cikin akushi ta kai fada, mutanen gari
da Sarki suka yi mamaki. Nan take Sarki ya amince zai aure ta.
Bayan ta koma gida sai aka gaya mata ta sanar da iyayenta, za a yi bikinta da Sarki. To da yake iyayenta duk sun rasu Marainiya ce, ba ta da kowa, da ta koma gida dare ya yi ta kwanta, sai ta tashi tsakar dare tana kuka domin tana tunanin ba wanda zai yi mata kayan gara.
Tana cikin wannan hali na damuwa, sai ta ga kwatsam tsobuwar nan ta ɓullo mata a tsakiyar ɗaki. Kuma ta tambaye ta ko mene ne yake damun ta.
Sai Marainiya ta yi mata bayanin dukkan abin da yake damun ta, har ya zamanto ba ta iya barci. Da 'ytar tsohuwa ta lallashe ta sai kuma ta gaya mata za ta kawo mata dukkan abin da take buƙata.
Yarinya ta yi ajiyar zuciya cikin Murna, ta yi wa tsohuwa
godiya. Tun kafin gari ya waye, sai ta ga ɗakinta cike da kayan gara fiye da
yadda take zato za ta samu, ta yi ta murna. Ta gode wa Allah.
Ana nan, ana nan, ranar bikinta da Sarki ta zo, aka ɗaura musu aure, aka yi gagarumin biki ya ƙare sai tsohuwa ta sake ɓullo mata a ɗakinta, ta kuma kawo mata kayan alatu da na marmari.
Ta ce mata kullum
za ta rinƙa kawo mata kayan daɗi ta rinƙa ba Sarki, amma kada ta gaya wa kowa.
Yarinya ta ce ba za ta gaya wa kowa ba.
Suka yi sallama tsohuwa ta tafi.
Bayan 'yan kwanaki sai matan Sarki suka fara tsegumi cewa amarya ba ta da kowa,
amma kullum Sarki yana ƙara son ta fiye da sauran matansa, kuma kayan alatu da
take ba Sarki wa yake ba ta? Suka yi ta bincike, amma ba su gano bakin zaren
ba, sai suka haƙura, suka bar ta.
To shi Sarki bai taɓa haihuwa ba, duk sanda matansa suka ɗauki ciki, sai ya zube. Rannan bayan 'yan shekaru da auren Marainiya da Sarki, sai ya tara matansa, bayan ya tabbatar kowacce tana da ciki. Ya ce da su kowacce ta tafi gidan mahaifinta sai ta haihu ta dawo. Ita kuwa marainiya sai ta tafi gindin wata tsamiya ta zauna, ta kama kuka, tana waƙa tana cewa,
wa zai ba ni yaro a yau?
Wa zai amshi haihuwa a yau?
Ni ba ni da uwa, ni ba ni da uba?
Tana cikin wannan hali sai tsohuwa ta zo ta sake tambayar ta abin da yake damun ta. Sai ta kwashe labarin yadda suka yi da Sarki ta gaya mata.
Sai tsohuwa ta ɗauke ta, ta kai ta gidanta, ta
ci gaba da kula da ita, tana yi mata albishir cewa in Allah ya yarda, za ta
haihu, cikin ba zai zube ba.
Suna nan tare da tsohuwa har ranar
haihuwa ta zo, ta haifi ɗanta lafiyayye, kowa ya gan shi ya ga ubansa. Amma
sauran matan Sarki kuwa ba su sami haihuwa ba, sai ɗaya daga cikin kishiyoyinta
ta sami labarin haihuwar amaryar Sarki Marainiya.
Sai ta fara bin ta a sace, har ranar
da aka sa za su koma gidan Sarki. Rannan sai amaryar Sarki ta tafi bakin rafi
don ta yi wanka tare da ɗanta. Da ta je bakin rafin sai ta ajiye jaririn, ta
shiga wanka. Sai kishiyar nan ta zo ta sace yaron, ta gudu da shi.
Da suka koma fada sai amaryar Sarki Marainiya
ta je ta gaya wa Sarki cewa ta haihu, amma an sace abin da ta haifa. Sai aka ƙi
yarda da wannan magana. Da kishiyarta wadda ta sace yaron ta zo, sai suka ce
ita ce ta haifi yaron.
Ita kuwa matar Sarki Marainiya sai
aka sa fadawa da yaran Sarki suka kafa mata ɗaki irin na dawaki, aka ajiye ta a
can, bisa cewa ta yi wa Sarki ƙarya. Da kishiyarta ta ba yaron nono sai ya ƙi
kamawa. Aka yi juyin duniyar nan, jaririn nan ya ƙi shan nono, sai aka rinƙa ba
shi madarar shanu, har ya girma.
Ana nan, ana nan, wata rana sai ɗan duba wato Sarkin bokayen Sarki, ya gaya wa Sarki cewa wannan ɗa nasa matar da ta rene shi ba ita ce uwarsa ba.
Mamaki ya kama Sarki, sai ya nemi Sarkin bokaye da ya gaya masa ta yadda zai gane uwar yaron. Sai mai duba ya ce ya tara matansa ranar kasuwar garin, kuma a tara mutane a fada, sannan duk matansa su yi abinci, su kawo shi bainar jama'a, kuma su jeru a fada.
Idan an yi haka, sai
a ce da yaron ya zaɓi abincin da matan Sarki suka kai wurin, to duk abincin da
yaron ya zo ya ci, tabbas mai wannan abinci ita ce uwarsa.
Ba tare da nuna shakka ba, Sarki ya ce a yi haka ɗin. Sarki ya umarci matansa a kan abin da ake so kowacce ta yi. Duk matan suka yi dafe-dafen kayan daɗi. Ranar kasuwa ta zo, mutane suka taru, fada ta cika ta batse. Amma ita amaryar Sarki Marainiya, kuma uwar yaron ta gaskiya, ba ta da abin da za ta dafa. Hasali ma tun ranar da aka kai ta ɗakin dawaki ba ta cin komai sai in an zuba wa doki dusa ta ɗiba, ta dama ta sha, ko ta yi tuwo da ita.
Da aka ce har ita ma sai ta yi abinci, sai ta ɗebi dusar da
aka kai wa dawaki kamar yadda ta saba, ta kama gafiya ta yanka, ta gyara ta da
kyau, ta ɗauka ta kai fada.
Da ta isa fada sai ta tarar duk sauran matan Sarki sun jeru, suka shiga yi mata kallon reni da nuna mata ƙyama. Can da ɗan Sarki ya zo a kan doki aka ce ya zaɓi abincin wadda zai ci daga cikin matan Sarki, sai kawai ya karya linzami ya doshi inda mahaifiyarsa Marainiya take. Da zuwa sai ya kama cin abincin dusar nan da ke gabanta.
Da mutanen da
suka yi cincirindo a fada suka ga haka, sai mamakin yadda al'amarin ya kasance
ya kama su.
Da Sarki ya ga alama lallai gaskiya
ce ta yi halinta, sai ya sa aka kama matar da ta yi satar yaron ta ce nata ne,
aka fille mata kai. Ita kuwa mahaifiyar yaron ta gaskiya sai Sarki ya ba ta haƙuri,
ya nemi ta gafarta.
Ba a daɗe da yin wannan abun ba, Sarki
ya kamu da rashin lafiya, wadda ta zama ta ajalinsa. Bayan an gama zaman
makokin rasuwar Sarki, sai aka naɗa ɗan Marainiya a matsayin sabon Sarki. A
cikin ikon Allah yaro ya hau karagar mulki. Ya ci gaba da tafiyar da harkar
mulki kuma 'yar tsohuwar nan da uwarsa zumuncin da yake tsakaninsu ya ƙara ƙarfi.
Ƙurunƙus.
Darasin dake cikin Tatsuniyar
- Alheri danƙo ne ba ya faɗuwa ƙasa bamza.
- In Allah ya rufa maka asiri, ba mai tonawa.
- Ƙarya fure take ba ta 'ya'yan.
0 Comments