Talla

Tatsuniyar Wani Sarki Da Matarsa

Daga: Aminu Abdullahi Muh’d

Ga ta nan, ga ta nanku.

Wani Sarki ne yana da mata uku, amma Allah bai taɓa bashi haihuwa ba. Wata rana sai ya nemi shawarar fadawansa a kan abin da ya kamata ya yi, saboda wannan rashin haihuwa. Sai suka ce ya kamata ya ƙara aure. Shi ko ya ɗauki shawararsu, ya sa aka nema masa budurwa kyakkyawa ya aure ta.

Bayan wasu ‘yan watanni sai Allah ya ba ta ciki, labari kuma ya game ko ina, matar Sarki tana da ciki. Su kuwa kishiyoyinta sai suka shiga baƙin ciki, don sun daɗe a Gidan Sarki ba tare da ko ɗaya daga cikinsu ta samu ko da ɓatan wata ba.

Daga nan sai suka shiga neman hanyar da za su bi su zubar da cikin, amma abu ya gagara, har lokacin haihuwa ya zo.

Lokacin da suka tabbatar ta kusa haihuwa, sai suka je wurin Sarki suka nemi izini su je shan iska da saran itace a jeji tare da bayinsu.

Ba tare da wani mugun zato ba, sai Sarki ya basu izini, amma da sharaɗi, ba za su je da amaryarsa mai juna biyu ba.  Sai suka ce ai zasu kula da ita, kuma babu abin da zai same ta.

Da suka nace, sai Sarki ya bar su suka tafi jeji da ita, a dajin nan naƙuda ta kama ta, suka kai ta gindin bishiya, suka kwantar da ita, ta haihu. Da suka ga ta haifi ‘ya kyakkyawa, kuma bata cikin hayyacinta, sai suka ɗauki jaririyar suka jefa a kan bishiya.

Can da rana ta yi sanyi, sai su da bayinsu suka kama hanyar gida, tare da mai jego. Lokacin da suka isa gida, sai Matan Sarki suka je turakarsa, suka gaya masa wai matarsa ta haifi wani ɗan itace ne, ba mutum ta Haifa ba.

Da jin wannan bayani sai ya fusata, domin ya ɗauka gaskiya suka gaya masa, ya sa aka kai amaryarsa wani gida ita kaɗai inda ba kowa, sai abin tsoratarwa, aka bar ta a can. Bayan wasu ‘yan watanni sai Bayin Sarki, suka je daji yanko wa dawakin Sarki ciyawa.

Suna cikin yankan ciyawa sai wata ‘yar tsuntsuwa ta zo ta sauka a kan bishiya, ta iske da ‘yar yarinya. Sai ta fara waƙa tana cewa,

Ɗan tsuntsu kar ka faɗa kan ‘yar Sarki,

Wadda kishiyoyi suka ce,

Wai ɗan itace uwarta ta haifa,

Suka jefa ta kan bishiya,

Ba ɗan itace ba ne,

‘yar Sarki ce.

Ta rinƙa maimaita wannan waƙa, har Bayin Sarki suka ji waƙar ‘yar yarinya ta kan bishiya. Wannan ya sa suka fita da gudu, suka koma gari.

Washe-gari ma da suka koma yankan ciyawa sai suka ji waƙar. Da suka kasa kunnuwansu da kyau, suka kuma saurari waƙar ‘yar yarinya, sai suka koma gida suka gayyaci mutanen gari masu yawa, domin su ma su je jejin su ji. Mutanen gari suka saurari waƙar da tsuntsuwa ke yi wa yarinya.  Daga nan fa suka koma gari, suka je suka sanar da Sarki abin da suka ji.

Sarki ya tashi da kansa ya nufi jeji inda yarinyar take, ya sa aka hau bishiya a ga ko me yake yin wannan waƙa. Da aka hau bishiya sai ga yarinya kyakkyawa mai kama da Sarki, sai ka ce kakin ta ya yi.

Bayan an sauko da ita Sarki ya gan ta, nan da nan ya rungumi ‘yarsa, yana ta salati irin na godiya ga Allah, yana sumbatar yarinyar nan, don ƙauna irin ta ‘ya da mahaifi. Bayan wannan nuna murna ta Sarki da amsar barka da arziƙi daga jama’arsa da ke wurin, sai ya sa aka kawo masa doki, shi da ɗinbin jama’a suka kama hanyar gari.

Da suka isa gida sai ya aika aka kawo masa uwar yarinyar da aka kai can wani gida da ke bayan gari, yana cike da nadama, amma kuma a cikin muryar bayyana farin ciki, ya ba amaryar haƙuri, ya nemi ta yafe masa horon daya yi mata ba tare da laifinta ba, a sakamakon makircin kishiyoyinta.

Bayan fada ta cika ta batse da mutanen gari, sai aka bayyana musu miyagun halaye da makircin sauran matan Sarki, da yadda suka sa Sarki ya hori matarsa ba tare da ta yi laifi ba, da  kuma yadda suka jefar da ‘yar Sarki a daji. Nan take Sarki ya umarci Hauni ya fille masu kawuna, aka je aka zuba su a rami, aka binne.

Sarki kuma ya ci gaba da sabuwar rayuwa shi da amaryarsa da ‘yarsa.

Ƙurunƙus.

Darussan Dake Cikin Tatsuniyar

  • v  Mugun nufi baya kashe ɗan kurciya.
  • v  Ƙaiƙayin ya koma kan masheƙiya.

Post a Comment

0 Comments