Dada: Aminu Abdullahi Mohd
Ga ta nan, ga ta nanku.
Wata rana wata mata mai juna biyu ta
je ɗibar ruwa a bakin rafi. Bayan ta cika tulunta da ruwa, sai ta kasa ɗauka
saboda cikinta ya girma sai nishi take yi, abin tausayi. Kuma ga shi ita kaɗai
ce ƙwal a wurin.
Haka ta haƙura ta zauna. Can sai ga
wani mutum ya taho, sai ta dube shi ta ce, "Malam don girman Allah ka ɗora
ni mana. "
Sai ya ce shi ba zai ɗora ta ba sai
dai idan za ta yi masa wani alƙawari.
Mai ciki ta dbe shi ta ce, "Na mene ne?”
Shi ko ya ka ɗa baki ya ce,
"Idan kin haihu, in namiji ne to abokina ne, idan kuma mace ce, to matar ɗana
ce." Da jin wannan sharaɗi sai ta yarda. Ya ɗauki tulu ya ɗora mata ta
kama hanya ta tafi gida. Da ta je gida sai ta yi wa mijinta bayanin yadda suka
yi da mutumin. Da yake mijinta mai sauƙin kai ne, sai ya ce, "To shi ke
nan, Allah ya sauke ki lafiya."
Bayan 'yan Kwanaki sai mutumin ya
zagayo gidan matar, suka gaisa. Ya nuna mata ɗansa suka yi sallama ya koma
gida. Bayan wata ɗaya sai matar ta haifi 'ya mace, amma jikinta na jaki ne. Da
mutumin ya ga haka sai ya yi halin dattaku ya ce, "To shi ke nan tun da an yi alƙawa ai sai an
cika."
Sai ya kira ɗansa aka ɗaura musu
aure da yarinyar ya kai ta gidansu. Yaro ya zauna da mace mai jikin kaki, ya ɗaure
ta a gida. Amma duk sanda ya tafi gona idan ya dawo gida sai ya tarar an yi
masa shara, an dafa masa abinci an kuma kai masa ruwan wanka bayan ɗaki. Kullum
haka, sai abin ya fara baby shi tsoro tun da ba kowa a gidan.
Rannan sai ya je ya sami babansaya
gaya masa, amma sai baban ya ƙi kula shi sai ya kore shi.
To da ma yaron yana mutunci da wata
tsohuwa maƙwabciyarsa dangarsu ɗaya, sai wata rana ya zauna a gindin bishiya,
yana tunanin abin ma akin da ke samunsa.
Da tsohuwar ta gan shi a zaune haka,
sai ya kira shi ya ce, "Ɗan yaro me ke damunka ne?" Shi kuma sai ya
kwashe labari ya bai wa wannan tsohuwa. To da ma ashe tsohuwa tana ganin duk
abin da yarinya take yi idan ya tafi gona. Watau rikiɗa take yi ya koma
Kyakkyawar budurwa, ta shiga yi masa waƙa, ta yi shara, ta yi wanke-wanke, ta
dafa abinci, ya ɗebo ruwa a rijiya ta kai masa ban ɗaki. Duk bayan ya gama
kafin ya dawo sai ta mayar da jikinta na kaka, ta ɗaure kanta a turke.
Da tsohuwar ya gama bai wa yaron
labarin abin da take gani sai ta shawarce ce da cewa gobe ya kwashi kayan aiki
kamar zai tafi gona, idan ya kama hanya sai ya ratse a hanya, ya zagayo
gidanta. Bayan sun gama shirya zancensu, sai ya koma gida yana mamaki, ya shiga
ɗaki ya kwanta.
Da gari ya waye sai ya saka kayan
aiki ya ɗauki fartanyarsa ya Kama hanyar gona. Bayan ya tafi ya yi nisa sai ya
ratse cikin ciyawa, ya zagayo ya gidan tsohuwa, ya same ta a ɗaki.
Daga nan sai suka ɓuya suka shiga leƙen
yarinyar. Jim kaɗan sai suka ga ta rikiɗa ta koma Kyakkyawar mace, ya fara waƙa
ta kama shara da sauran ayyukan gida, ta shirya miya, ta dafa abinci, ya zuba
nasa, ya kai masa ruwan wanka ban ɗaki.
A daidai lokacin da ya fito daga
bayan gida sai mijinta ya tsallaka danga ya dira a gabanta. Sai kawai ta razana
za ta rikiɗa sai ya kama hannunta ya fara yi mata waƙa yana roƙon ya.
Da ta ji waƙarsa sai ta fara kuka
tana roƙon ya yafe mata. Shi ke nan suka yi zamansu cikin daɗi suka ci gaba da
more rayuwarsu cikin ƙauna da farin ciki. Ɗan kan ɓarya, ba domin Gizo ba da na
sheƙa muku Ƙarya.
Ƙurunƙus.
Abubuwan Da Labarin Yake Koyarwa
Alƙawari kaya ne, in an ɗauka sai a
huta.
Tsintar dami a Kala.
Rabon kwaɗo ba ya hawa zama.
0 Comments