Talla

Tatsuniyar Dagaci Da Malaminsa

Daga: Aminu Abdullahi Mohd

Ga ta nan, ga ta nanku.

An yi wani Dagaci a wani gari yana da matarsa, to amma matar ba ta taɓa haihuwa ba. Ba tare da saninsa ba, wata rana matar wani babban malami ta je wurin matar Dagaci hira a gidansa. Suna cikin hjira sai matar Dagacin ta fara ba matar malamin labarin tashin hankalin da take ciki na rashin haihuwa. Kuma ga shi mai gidanta, watau Dagacin, y ace yana son ya sami ‘ya’yan da za su zo su gaje shi. Kuma ya ba matarsa wasu ‘yan watanni, idan ba ta sami ciki ba zai kore ta, ya auro wata matar. Wannan barazana ce fa ta sa matar Dagaci ta fara kuka da baƙin ciki.

Da matar malami ta ji yadda labarin yake, sai ta tausayawa matar Dagaci. Shi ken an, sai matar malamin  tace magta, “Kin ga ni yanzun ina da ciki wata biyu, sai ki fara dunƙula tsumma ki ɗaura a cikinki ki gaya wa mijinki cewa Allah ya ba ki juna biyu.”

Abin da matar malami take son yi shi ne idan Allah ya sauke tab lafiya, za ta kawo wa matar Dagaci abin da ta Haifa, domin ta nuna wa mai gidanta cewa ta haihu.

Wannan hikima ta farantawa matar Dagaci rai, kuma ta yarda akayi alƙawari da matar malami, har matarDagaci ta durƙusa tana yi mata godiya.

Bayan ‘yan kwanaki sai ta gaya wa Dagaci cewa ta yi ɓatan wata, kuma tana tsammani tana da ciki wata biyu. Da Dagaci ya ji wannan labari sai ya shiga murna. Ya fara faɗa wa fadawansa da mutanen gari cewa yanzu kam matarsa tana da juna biyu, kuma in Allah ya yarda bad a daɗewa ba za ta Haifa masa ɗan da zai gaje shi.

Saboda farin cikin da Dagaci yake yi, sai ya ba umarni a kai matarsa wani gyararren gida. Ya sa a riƙa yi mata duk abin da take so. Kumaya ce kada ta taka ko ƙofar ɗaki don kada ta wahala a lokacin da take renon cikin har ranar haihuwarta.

Ana nan sai mutane suka fara tsegumi a kan ai da ma matar Dagaci bat a haihuwa, yaya kuma yanzu za a ce tana da ciki? Surutai suka yi yawa a gari, har wasu suka bugi ƙirji, suka sami Dagaci suka fara yi masa irin wannan magana. Wani daga cikin su ya ce, idan matarDagacin nan ta haihu, to a ɗauki rumbun zuba amfanin gonar gidan Dagaci a ɗora masa a kansa. Wani kuma y ace, in ta haihu a ɗora masa igiya a kwankwaso a zagaya gari da shi har sai ya mutu.

Can na ukun su ya ce, in hart a haihu, to zai cinye buhun barkono  goma shi kaɗai. Wani kuma ya ce, shi idan ta haihu to zai cinye dutsen da yake bayan gari. Haka dai suka ci gaba da maganganu, shi kuwa Dagaci bai ce komai ba, aka ci gaba da renon ciki har ya kai lokacin haihuwa.

A ranar da matar malami ta haihu sai aka ce ai matar Dagaci ta haihu. Kamar yadda akayi alƙawari, sai matar malami ta ɗauki jaririnta ta kai wa matar Dagaci ba tare da wani yasan an yibn haka ba. Bayan labari ya bazu a gari sai masu rantsuwa suka dawo gaban Dagaci suka ce har idan an fito da yaro aka yi masa aski ranarsuna, to za su cika alƙawarin da suka ɗauka, amma idan kuma zancen ƙarya ne, to za a kashe matar Dagaci. Dagaci ya yarda da haka.

Matar Dagaci ta ci gaba da renon jaririn matar malami har ranar suna ta zo. Ana gobe suna sai matar malami ta dawo t ace mijinta ya ce shi ba zai ba da ɗansa ba, saboda haka a dawo masa da ɗansa. Matar Dagaci na jin haka, sai ta ce, “Haba matar malam, bayan mun ganma Magana da ke kuma kin ɗauki alƙawari yanzu ki dawo k ice ba zai yiwu ba, ai wannan cin amana ne. Idan Dagaci y ace ina jariri bayan kowa ya ji na haihu, to me zan gaya wa Sarki? Kuma an ce idan ba a fita da yaro ba gobe ranar suna, za a kashe ni. Ki yi min rai mana!”

Haka dai ta yi, ta yi, amma matar malami ta ƙi yarda, daga ƙarshe ta karɓi ɗanta ta tafi gida, matar Dagaci ta rasa yadda za ta yi. Da ta gab a mafita sai ita da ƙanwarta suka shirya za su gudu cikin dare. Da dare ya yi suka kama hanyar daji suna cikin tafiya, sai suka ji wata tsawa a gabansu sai suka ga ƙasa tat sage, sai ga wani jariri a cikin tsumma yana kuka.

Sai matar Dagaci ta yi godiya ga Allah, ta ɗauki yaro suka kama hanyargida. Ba su jima da komawa gida ba gari yaw aye.

Fada kuwa ta cika fal da mutanen gari da makaɗa da mawaƙa da wanzamai za ayi waɗ an Dagaci aski, kuma a raɗa suna. Su kuma masu alƙawari suna gefe suna jiran burinsu ya cika a ce babu yaro. Sai Dagaci ya tura  a akawo jariri. Aka shiga cikinn gida aka fito da yaro kyakkyawa mai kama da Dagaci. Nan take waɗanda suka ɗauki alƙawari idanu suka raina fata.

Shi kuma malami mamaki ya kama shi, aka dai yi wa yaro aski, aka raɗa masa suna. Sarki ya sa aka kamo waɗanda suka ɗauki alƙawari aka fara hukunta su, ɗai-ɗai da ɗai-ɗai, har suka mutu. Shi kuma malami ya kama hanyar gida ya kwashe labara ya gaya wa matarsa yadda aka yi.

Sai malami y ace da matarsda ta ɗauko yaron su ma su raɗa masa suna. Da te je ta ɗauko yaro, sai ta tarar ya mutu. Matar malami kuma baƙin ciki ya kama  ta, ta kama hanyar gidan Dagaci. Da ta shiga ta sami matarsa sai ta yi tab a ta haƙuri game da laifin da ta yi mata. Ita ko matarDagaci ba komai, zance ya wuce, ta ci gaba da zaman daɗi da mijinta har lokacin da mai rabawa ta raba.

Ga ɓera nan, ga ɓera nan, duk wanda ya ji tsoro alhaki a kansa.

Ƙurunƙus.

Abubuwan Da Labarin Yake Koyarwa

Ɗa kyautarAllah

Alheri ya fi mugunta. 

Post a Comment

0 Comments