Daga: Aminu Abdullahi Mohd
Ga ta nan, ga nanku.
Akwai wata budurwa mai suna Yakadi a wani ɗan ƙauye da ke nan kusa da bakin rafi. Wata rana sai mahaifanta suka aike ta lambu ta samo ganyen miya. Ta shirya ta kama hanya tare da ƙannenta, suka je, suka samo ganyen miya. A kan hanyarsu ta dawowa gida sai suka haɗu da wata tsohuwa ta ce dasu,
“Sannunku ‘yan mata, don girman Allah ku taimake ni da ganyen ɗan kaɗan mana.”
Sai ita Yakadi ta ce, “Ba za a bayar
ba.”
Suka ci gaba da tafiya, da suka kusa kaiwa kusa da wani dutse sai suka ce za su huta. Bayan sun zauna sun huta, sai ƙannenta suka tashi tsaye za a fara tafiya, amma ita Yakadi sai ta kasa tashi domin mazaunanta sun manne a jikin dutse.
Suka yi ƙoƙarin su ɓanɓare ta domin su tayar da ita amma suka kasa. Da suka gaji, sai suka bar ta a can, suka nufi gida da gudu don su sanar da iyayensu abin da ya faru.
Da iyayen suka ji haka,
sai suka kama hanya har inda 'yarsu ta maƙale. Suna isa, suka yi ta ƙoƙarin
ciro ta, amma abu ya gagara. Sai suka yanke shawarar gina mata ɗaki a nan, haka kuwa aka yi. Tana can, kullum
suna kai mata abinci.
Duk sanda mahaifiyarta ta je wurinta
a ɗakinta, sai ta yi wata waƙa, in ta ji muryar mahaifiyarta ne sai ta buɗe
mata ƙofar ɗaki ta shiga, in kuma ta ji wata murya ce daban, sai ta ƙi buɗewa.
Haka ta ci gaba da rayuwa har zuwa wani lokaci da Kura garin yawo ta tarar da ɗakin da Yakadi ke ciki, ta yi ƙoƙarin shiga, amma ta kasa.
Ana nan, wata rana Kura ta ɓuya, ta ji irin yadda uwar
yarinya take yin waƙa a buɗe, ta shiga. Bayan uwar yarinyar ta tafi, sai Kura
ta je ta yi waƙar, to amma da yake muryar ba irin ta uwar yarinyar ba ce, sai
ta ƙi buɗewa.
Da Kura ta ga haka, sai ta tafi inda
ake gyaran murya, aka gyara mata. A kan hanyar zuwa inda Yakadi take, sai yunwa
ta kama Kura. Da ta ga ƙuda, sai ta kama shi ta haɗiye.
Da Kura ta isa ƙofar ɗakin, ta fara
waƙa sai muryarta ta shaƙe, ta koma kamar ba a gyara ba. Yarinya kuwa ta ƙi buɗe
ƙofa, Kura kuwa ta sake komawa wajen gyaran murya, mai gyara ya ce mata in ta
kama hanya kada ta ci komai, sai Kura yi waƙar ta gama. Sai Kura ta yarda, ta
kama hanya.
Kura tana cikin tafiya, sai yunwa ta
sake kama ta. Da ta ga sauro, sai ta kama shi, ta haɗiye. A nan ma muryar Kura
ta sake ɓaci, ta koma wajen masu gyara a karo na uku, masu gyara suka sake
gyara mata murya, suka haɗa ta da mai kula da ita har sai sun je bakin ɗakin da
yarinya take.
Da yake Kura ba ta ci komai a hanya
ba da ta yi waƙa a ƙofar ɗakin Yakadi, sai ta ji murya kamar ta mahaifiyarta,
ta ja ƙofa ta buɗe, Kura ta shiga ta cinye ta, amma ta bar kai da ƙafafu.
Bayan Kura ta tafi, sai uwar yarinya ta je, ta tarar an cinye 'yarta, in ban da kai da ƙafafu. Sai ta fara kukan baƙin ciki.
Tana cikin kuka sai tsohuwar nan ta zo ta rarrashe ta, kuma ta gaya mata
idan ta je gida ta ƙona kai da ƙafafun Yakadi ta zuba tokar a ƙwarya mai yoyo,
idan tokar ta fara zuba sai ta rinƙa kiran sunayen gangar jikin Yakadi ɗaya
bayan ɗaya, har sai 'yarta, ta haɗu. Sai ta yi wa tsohuwa godiya, ta tattara
kai da ƙafafun 'yarta, ta koma gida.
Da ta koma gida sai ta yi yadda
tsohuwa ta umarci ta yi. Da ta fara kiran sunayen ɓangarorin jikin 'yarta, sai
duk ɓangaren da ta ambata ya faɗo, har dai ta gama kiran dukkan sauran sassan
jikin yarinya, sai ta ga 'yarta ta dawo da rai kuma Kyakkyawa kamar yadda take
a da, ta ci gaba da rayuwa har lokacin da aka yi mata aure.
Ƙurunƙus.
Darasin Dake cikin Tatsuniyar
- Kyautata zamantakewarku da al'umma da girmama na gaba daku.
- Alheri danƙo ne ba ya faɗuwa ƙasa banza.
0 Comments