Talla

Tasuniyar Marainiya

Daga: Aminu Abdullahi Muh’d

Ga ta nan, ga tananku.

Akwai wata yarinya Marainiya, wato wadda take ba uwa ba uba; kuma ita kaɗai ce a wurin mahaifiyarta, lokacin da mahaifanta suka rasu suka bar ta. Ta sha wulaƙanci wurin kishiyar uwarta, wadda take ‘ya’yan maza da mata, waɗanda duka suka taru a kanta suka riƙa yi mata wulaƙanci.

A cikin wannan yanayin kullum da sassafe takan je bakin wata kurna ta zauna ta yi ta kuka. Wannan kurna tana yin ‘ya’ya masu yawa, ga kuma zaƙi zaƙwai. Abincinta kenan daga safe har yamma, kuma idan za ta koma gida sai ta ɗebo waɗanda za ta ci da dare.

To akwai wani dan sarki kyakkyawa, mai suna Aminu, wanda ‘yar kishiyar uwarta take so, to amma shi baya sonta. Shi kuma ya kan je shan iska, ya hau kan wannan bishiyar kurna da Marainiyar take zama a bakinta, ta sha ‘ya ‘yanta, yana kallon kowa, amma babu wanda zai gan shi don ganyen bishiyar ya ɓoye shi.

Shi kenan, wata rana Marainiya tana nan zaune sai ɗan sarki ya sauko daga bishiya sai ya ce,

“Sannunki ‘yan mata.”

Sai ta ce,

“Yauwa samari”

Aminu ya ce,

“Me ke damun ki ne? Kullum sai in zo in ganki a bakin wannan bishiya, har tunanin da ki keyi baki sanin zuwana, kuma ga shi kikan riga ni zuwa don ni sai da la’asar nake zuwa, har in hau bishiya ba ki gani na’’

“To ya ka ke zama a saman bishiyar kurna mai ƙaya?’’

 Ta tambaye shi.

Sai ya ce,

“Ni na san dabarar da nake yi.”

Haka dai suka ci gaba da hirarsu har ya kawo ga maganar aure, sai ta ce,

“Ni dai Marainiya ce, ba ni da uwa, ba ni da uba.”

Sai ɗan Sarki wato Aminu ya ce,

“Yau na zama uwa da uba a wurinki.”

Gata nan har ya fara zuwa gidan su Marainiya. Da ‘yar kishiyar ta gane ɗan Sarki ne yake zuwa wurin Marainiya, sai ta ƙuduri cewa sai ta san makircin da za ta yi. Sai ta sayo allurai da yawa ta je ta sossoka a inda Aminu yake zama idan ya zo wurin Marainiya. Da zuwansa sai ya zauna a kan alluran nan, kuma gaba ɗaya alluran suka shiga jikinsa. Nan da nan ya fara jin zazzaɓi, ya tashi ya tafi gida. Ciwon ɗan sarki dai ya gagara warkewa, babu irin maganin da ba a yi ba.

            Wata rana Marainiya ta tafi ɗiban ruwa a rafi, sai ta ji aljanu suna maganar ɗan sarki ba shi da lafiya, amma da an samo kashin tsutsotsi masu cin mutane a bayan wani gari mai nisa, aka jiƙa masa ya sha, to zai warke.

            Da Marainiya ta ji, sai ta yi maza ta ɗauki goranta, ta je gida, ta aske kanta ta shafe jikinta da baƙin tukunya, ta sauya kayan maza, ta ɗauki kwano, kamar almajiri zai je bara.

            Ta kama hanyar wancan gari mai nisa, inda za ta samo ƙashin tsutsotsi mai cin mutum, har sai da ta yi tafiyar shekara biyu kafin ta isa garin.

Sai ta je wurinsu a hankali, ta kwanta don in sun ji motsin tafiyarta za su cinye ta. A hankali ta yi ta lalubowa ɗaiɗaya.  Bayan ta samu abin da  ta je nema, sai ta kama hanyar dawowa garinsu, ta isa lafiya.

            Bayan ta ɗan huta, sai ta kama hanyar zuwa gidan sarki, ta tarar mutane maƙil sun cika  fada suna jiran mutuwar Aminu. Da zuwa fada sai ta fara bara, mutane sun ɗauka namiji ne, suka ce,

“Kai kana ganin ɗan sarki babu lafiya amma sai ka zo ka yi mana bara don baka da kunya?” 

Sai ta ce,

Kubar ni in duba shi ko zai warke, akwai wani magani da nake tafe da shi.”

Sai suka dakawa ɗan almajiri tsawa, suka ce,

“Duk duniyar nan babu wanda zai warkar da shi kai?”

            Sai ta ce,

“A bar ni mana in ɗan gwada.”

            Da ƙyar aka bar shi ya shiga, da shiga sai ta ciro wannan kashin tsutsa, ta jiƙa, ta ba ɗan sarki, ya sha. Cikin ikon Allah nan take sai ya fara amai, duk ya amayar da ciwon da ke damunsa, ya warke sarai, kowa yana mamakin ɗan almajiri.

A cikin farin ciki sarki ya ce,

“Zan ba ka gida da dawakai  da dukiya mai yawa,”

Shima sarki  bai san da mace yake magana ba.

Sai ta ce,

“A’ a ba na son wannan”

Sai sarki ya ce,

“To me ka ke so?”

Ba tare da ɓata lokaci ba, Marainiyar da ake zato namiji ce ta ce,

“Ni dai babu abin da nake so kamar zoben hannunsa.”

Ɗan sarki Aminu bai taɓa zaton zai rabu da wannan zobe ba, amma sai ya cire yaba ta.  Ta karɓa ta tafi.

Bayan kwana biyu sai ya je gidansu Marainiya a cikin fushi, ya ce da ita,

“A duk garin nan babu wanda bai san da rashin lafiyata ba, amma ke ba ki taɓa zuwa gani na ba.”

A cikin tattausar murya takalle shi ta ce,

“Zauna ka ji labari”

            Ya zauna ta fara faɗa masa yadda ta yi. Da ta gama sai ya ce,

“Karya ne, idan maganarki gaskiya ce, to me aka bai wa ɗan almajirin?”

Sai ta ce,

“Zobe.”

Y a ce, 

“To idan ke ce, nuna mani zoben,”                                                           

Sai ta ɗauko taba shi. Ya duba zobe, ya tabbatar zobensa ne. Daga nan ya fara mamaki. Ya ɗauke ta suka je gaban babansa, suka gaya masa labarin abinda ya faru. Ya sa aka ɗaura masu aure, aka yi gagarumin biki, kuma aka basu kyautar gari guda da dukiya mai tarin yawa, suka ci gaba da cin duniyarsu da tsinke.                                                                     

Ƙurunƙus.

Darasin Dake Cikin Tatsuniyar

  • v  Rabon kwaɗo ba ya hawa sama, zai ya faɗo qasa kwaɗo ya ɗauki abun sa.
  • v  Mai nema yana tare da samu, nema baya tashi hana nan.
  • v  Mai rabon ganin baɗi ko ana ha maza ha mata sai ya gani.
  • v  Hassada ga mainrabo takice, sai mai hassada ya gama hassadarsa.

Post a Comment

0 Comments