Talla

Tarihin Aliku Dangote Fitaccen Dan Kasuwa Ɗan Asalin Kano

 

Daga: Bello Hamisu Ida


17 Satumba, 2021

KANO, NIJERIYA — An haifi Aliku Dangote GCON a ranar 10 ga watan Afrilu shekara ta 1957 ya fito daga Jihar Kano dake Ƙasar Nijeriya. Shi ne shugaban Dangote Group, mutumin da ya fi kuɗi a Afrika wanda ke da zunzurutun kuɗi har dalar Amurka Biliyan Sha Biyu US$12.7 a ƙididdigar da aka yi ta watan Satumba 2021.

Abun alfahari ne a samu babban mutum Bahaushe, Musulmi ɗan asalin Jihar Kano a Arewacin Nijeriya, mahaifinsa Mohammed Dangote da mahaifiyarsa Maryam Sanusi Dantata sanannu ne, mahaifiyarsa ɗiya ce ga Sanusi Dantata sananne mai kuɗi a Nijeriya, wato dai shi Dangote jika ne ga Alhassan Dantata, shi ma Alhassan Dantata ya taɓa zama wanda ya fi kowa kuɗi a Yammacin Afirika.

Dangote ya fara karatunsa a makarantar Sheikh Ali Kumasi Madrasa, daga nan ya wuce Capital High School duk a garni Kano.

Ya taɓa cewa,

“Lokacin ina yaro, ina makarantar Firamare, na kan je in sayi katan ɗin alewa in saida don in samu kuɗi. Ina da sha’awar kasuwanci sosai ko a wancan lokacin”.

A shekarar 1978 ne ya kamala makarantar Goɓernment College, Birnin Kudu,  daga nan ya wuce makarantar Jami’ar ta Al-azhar dake Cairo inda ya samu kwalin Digiri a kan Kasuwanci da Gudanarwa.

Dangote ya kafa kamfaninsa wanda ya sanya wa sunan Dangote Group a garin Kano a matsayin ƙaramin kamfani a shekarar 1977, a shekarar ne ya koma Legas da zama don faɗaɗa kamfaninsa. A yau kamfanin ya mallaki tiriliyan da yawa tare da faɗaɗa ayyukansa a garuruwan Benin da Ghana da Nijeriya da Zambia da Togo. Dangote Group ya shahara wajen yin aikin sarrafa abinci tun daga samar da sminiti da jigilar kaya, haka kuma, Dangote Group ya mamaye kasuwancin Sukari a Nijeriya. Kamfaninsa ya koma babban rukuni na masana’antu a Nijeriya da suka haɗa da Dangote Cement da Dangote Flour da Dangote Sugar Refinery.

A watan yuli na shekarar 2012, Dangote ya tuntuɓi Hukumar Kula Da Tashoshin Jiragen Ruwa ta Nijeriya don ya ba da hayar wani fili da aka yi watsi da shi a tashar ruwan Apapa, wanda aka amince da shi. A shekarar 1990, ya tuntuɓi babban Bankin Nijeriya da ra’ayin cewa zai fi arha bankin ya baiwa kamfanin sufurinsa damar sarrafa motocin ma’aikatunsu wato Bus, shawarar da ita ma ta karɓu sosai. Ya kuma bayar da gudummuwar kuɗi ga Ma’aikatar Wasanni ta Nijeriya don gyara filin wasanni na ƙasa da ke Abuja.

A Kano da Nijeriya da Afrika, a yau Kamfanin Dangote Group na da rinjaye a kasuwar sukuri, haka kuma, shi ne ke samar da kashi 70 na kasuwanci. Matatarsa ta Dangote Group ita ce matata mafi girma a Afrika, kuma matata ta uku mafi girma a duniya, tana samar da Tan 800, 000 na sukari a duk shekara.

Dangote Group ya mallaki masana’antar gishiri da masa’antar fulawa kuma shi ne babban Kamani mai shigo da shinkafa da kifi da taliya da sminiti da taki. Kamfaninsa yana fitar da auduga da goro da koko da irin sesame da ginger zuwa ƙasashen waje. Dangote Group yana da manyan jari a cikin gidaje, banki, sufuri, masaku, mai, da iskan gas. Kamfanin yana ɗaukar ma’aikata fiye da dubu sha ɗaya kuma shi ne babban kamfani na masana’antu a Kano da Nijeriya da Afrika baki ɗaya.

Aliku Dangote yana zaune a garin Lagos dake Nigeriya, ya taɓa aure sau biyu amma sun rabu da matayensa. Yana da ‘ya’ya guda uku: Mariya Aliku Dangote da Halima Aliku Dangote da Fatima Aliku Dangote, haka kuma yana da ɗan riƙo mai suna Abdulrahman Fasasi. Ɗan uwansa Sani Dangote ya rasu ranar 14 ga watan Nuwamba, 2021.

Za a ci gaba…

 

Post a Comment

0 Comments