19 Disamba, 2021
Sojojin sun tashi maɓoyarsa ne suka kuma kashe ƴan ta’adda da dama a dajin Zamfara da Sakkwato.
Sojojin sun illata jagoran ƴan ta’adda wato Bello Turji, kuma akwai yaƙinin cewa an raunata shi lokacin da jiragen yaƙin sojoji su ka kai hari maɓoyarsa.
Jaridar PRNigeria ce ta faɗi labarin da ta samo a wata ta majiya da ga ɓangaren jami’an tsaro.
Rahoton ya ƙara da cewa, jiragen yaƙin rundunar dakaru ta Sintirin Haɗin Kai sun hallaka ƴan fashin daji a Zamfara da Sakkwato da safiyar Lahadi nan.
Majiyar ta tabbatar da cewa Sojoji sun kai hari ta sama da ta ƙasa a Shinkafi, Bafarawa, Isa da kuma Sabon Birni.
Zuwa yanzu, ba a tantance adadin ƴan ta’addan da a ka kashe ba.
PRNigeria ta ji cewa sauran yan fashin da su ka samu raunuka, sun gamu da ajalinsu a hannun sojojin ƙasa.
Garuruwan Katsina da Kaduna da Zamfara da Sokoto da Kebbi da Niger da Taraba na fama da hare-haren ƴan bindiga.
Ko a ranar sha huɗu ga watan Disamba sai da aka tsinci wata takarda da ake zargin cewa Bello Turji ne ya rubuta, duk da yake ba a san ingancin takardar ba, amma ana zargin cewa Bello Turji ya rubuta takardar domin neman afuwa da al'umma da Gwamnan Zamfara da shugaban ƙasa.
0 Comments