ABUJA, NIJERIYA - Shugaban
Nijeriya Muhammadu Buhari ya ƙi sanya
hannu a kan ƙudurin dokar da 'yan
majalisar dokoki suka amince da shi domin yin gyara ga dokar zabe ta 2021 wadda
zata bayar da dama yin zaɓen ƙato-bayan-ƙato.
A wasiƙar da shugaban ya rubuta wa Shugaban Majalisar
Dattawa Sanata Ahmed Lawan, ya tabbatar da cewa;
‘Irin matsalolin
da Ƙasar ke fuskanta ya sa ba
zai sanya hannu kan wannan ƙudurin
ba’.
Daga
cikin dalilan da ya bayyana, Shugaba Buhari ya ce zunzurutun kuɗin da zaben ƙato-bayan-ƙato zai ci, da kuma ƙalubalen tsaro da za a fuskanta wurin gudanar da
shi na daga cikin abubuwan da ya duba waɗanda suka hana shi saka wa ƙudurin hannu.
Haka kuma,
ya yi batun da haƙƙin 'yan
ƙasa suke da shi da kuma cire
ƙananan jam'iyyu daga
tafiyar. Da kuma batun zaɓen fid
da gwani ta hanyar 'yar tinƙe, shi
ne babban abin da ya janyo taƙaddama
a gyaran-fuskar da aka yi wa dokar zaɓen.
Matakin
na shugaban ƙasa ba dole ne ya yi wa wasu
daga cikin 'yan majalisar daɗi ba. Saidasi
Shugaba Muhammadu Buhari ya jaddada wa majalisar cewa ba zai yi gaban kansa ba wajen
ɗaukar wannan mataki.
Wasu 'yan
majalisar sun fara kunfar baki bayan da suka ji shiru daga Shugaban ƙasar, yayin da wa'adin da yake da shi na sanya wa ƙudurin dokar hannu ya wuce.
0 Comments