Talla

Rigima Tsakanin Wasu Jaruman Tiktok Ya Janyo Zubar Da Jini

Daga: Hauwa’u Bello

30 Disamba, 2021

ABUJA, NIJERIYA  Faɗan Sudeenly da Aisha Zaki a manhajar Tiktok ya ja zubar da jini a tsakaninsu. Manhajar Tiktok dai ta shahara sosai wajen yaɗa bidiyo inda mutane ke zuwa suna ɗaukar bidiyo tare da watsa shi a cikin duniya. Faɗa sakanin Sudeenly da Aisha ya fara ne bayan wani bidiyo da aka gani a Tiktok, a cikin bidiyon an ga wasu mata suna bugun Sudeenly a cikin wani gida inda ake tsammani a gidansu Sudeenly ne.

A cikin bidiyon an ji muryoyin wasu mata inda wata ke cewa,

“Don rashin mutunci a gaban babarta?”

An ƙara jin wata murya wadda aka yi zaton ta Sudeenly ce inda take cewa,

“Mama”

Wannan bidiyo ya kara hura wutar gaba a tsakanin mabiyan Sudeenly da Aisha. Daga baya kuma ita Aisha ta sake yin wani bidiyo inda take iƙirarin cewa, Sudeenly bata ga komai ba, ita kuwa Sudeenly ta faɗi cewa bata tsoron kowa a Tiktok.

Bayan wannan taƙaddamar sai aka ga bidiyon Aisha duk jini a jikinta, tana zaune cikin mota, tana numfashi sama-sama ga alama asibiti za a kai ta,  an ji muryar wata mata na cewa,

“To jama’a kun ga dai har gidansu taje ta yi mata wannan abun, Sudeenly ‘yar Fashi ce”.

Waɗannan bidiyo guda biyu sun ƙara asassa fitina kamar wutar daji a manhajar Tiktok inda wasu ke ganin abun ya yi tsanani a tsakanin matan guda biyu. Wasu na goyon bayan Aisha Zaki wasu kuwa na goyon bayan Sudeenly, duk matan guda biyu dai suna da ɗimbin mabiya masu tarin yawa.  

Kodayake, wasu mabiyan Aishar har waƙa suka yi wadda ke nuna yadda Sudeenly ta sha duka a hannun Aisha. Wannan da ma wasu masu bibiyar ‘yan matan guda biyu sun ƙara tunzura wutar gabarsu da kuma ƙara asassa faɗa a sakaninsu.

Ba Sudeenly da Aisha ne kaɗai ke faɗa a kafar sadarwa ta Tiktok ba, akwai wasu matasa da manyan mata da suke faɗa da zage-zage da aibunta juna a cikin kafar don nuna goyon bayansu ga Aisha ko Sudeenly, ga alama muryoyin manyan matan da suke goyon bayan Aisha ko Sudeenly ko dai mahaifansu ne ko kuma ‘yanuwansu na kusa.

A cikin wani Akawu na Tiktok na @queenkhady22 an ji wata murya inda ake cewa,

Ke Aisha Zaki, na bada awa ashirin da huɗu a nemo mani ke, da mahaifiyarki…

An kuma ƙara jin wata murya a akawun ɗin @jawaheer_sarki, inda ake cewa,

Sudeenly kin ce duk wanda ya zage ki sai kin hana shi yawo a Kano ko? Kuma sannan duk wanda ya zage ki a Soshiyal Midiya sai kin zo har gida...

Haka kuma an ƙara jin wata murya a akawun ɗin @daddy_yunny inda yake cewa,

An ji labarin cewa Sudeenly ta bayyana kuma ta je Station ɗin da ta rufe Aisha Zaki ta samu aka bada beli na Aisha Zaki…

Ire-iren waɗannan muryoyi sun ƙara asassa wutar gaba a kafar sadarwa ta Tiktok. Mutane da dama dai na ganin cewa Manhajar bata da wani amfani bayan yaɗa alfasha a tsakanin matasa. Duk dayake dai wasu daga ciki masu amfani da manhajar suna ƙoƙarin yaɗa abubuwan alƙairi a cikin manhajar.


Post a Comment

0 Comments