Talla

Musa Bello Galadunchi: Katsina babu Dan Siyasa kamar Muntari Lawal

Daga: Musa Bello Galadunchi
21/12/2021

KATSINA, NIJERIYA - Alhaji Muntari Lawal ya taɓa cewa,

"Idan muka kulle ƙofa daga ni sai Gwamna, yana jin ra'ayina a siyasance, amma idan a waje ne, to dole ra'ayinsa zan faɗi, amatsayinsa na shugaba, shugabanci ba wasa bane. " 

Ya fadi haka ne, game da maigidansa, Mai girma Governor, Rt. Hon. Aminu Bello Masari. Yana nufin baya da wani ra'ayin kansa madamar ya saɓawa ra'ayin Governor. Kuma haka ya kamata kowane mabiyi ya mu'amalanci shugabansa in dai a bainar jama'a ne. Domin haka magabata suka mu'amalanchi shuwagabanninsu, wannan yana nuna tsantsar biyayyasa.

Sannan kuma ya ce,

 "Bin shi nike kamar makaho", 

Wato sai abinda ya ce, wannan baya nufin in daga shi sai shi ne, baya bashi shawarar data dace game da gudanar da al'amurran al'umma, kamar yadda hakan ta faru babu adadi.

Wannan ne yasa shi kansa Gwamnan babu wanda yake maida al'amurran siyasarsa gare shi kamar Alhaji Muntari Lawan, musamman lokatan da abubuwa suka rikece.

Ka taɓa ganin wanda ke da kusanci da Gwamna irin wannan bawan Allah? amma ka same shi baya kwaɗayin tsayawa takara, kai ba ma hakaba, ko maganar yin takarar kayi masa, sai kaga ranshi ya baci, anya muna da irin waɗannan mutanan kuwa?

Abaka wuka da nama, a kan fitar da tsari na zaɓen cikin gida na jam'iyya, amma kayi aikin nan ka gama, baka da wani zaɓin ƙashin kanka a ciki, mataki irin wannan, wanda wasu sun neme shi da kuɗinsu su don su samu wannan dama, amma basu samu ba!

Da ace zai nemi takarar Gwamna, tun daga wannan dama da ya samu zai tabbatar da cewa ya dasa mutanansa, don kuwa hakan ya bashi damar samun tikitin takarar Gwamna na Jam'iyyar, amma ina, ba wannan bane gabanshi. Tunda kake ka taba ganin haka a siyasar Jihar Katsina?

Ko a nan kaɗai aka tsaya, baka iya kawo wani mutum, mai irin wannan kusancin wajen Gwamna, ya samu wannan damar, kuma ya barta ta tafi haka nan, Allah ya yawaita mana irin wannan bawan Allah a Jihar Katsina.

To ba nan kaɗai abin ya tsaya ba, shi ne mutum ɗaya tilo wanda a tarihin siyasar Katsina, ya yi fito na fito da badaƙalar cin hanci dake tattare da aikin Hajj.

Kowa yasan rahoton da ya fitar, bayan an kammala aikin Hajji, lokacin da mai Girma Gwamna ya bashi ragamar Amirul Hajj a 2018, karanta sakamakon da ya fitar, wanda babu yadda ba ayi ba, a hana fitar da wannan sakamakon, amma ya fitar dashi. Tun wancan lokaci zuwa yau, baka da wanda ya nunama wannan sakamakon yatsa, da sunan rashin amincewa, madamar mutum gaskiya yake so, to Gwamna kansa da ya ga rahoton, hawaye ya rinƙa zubarwa.

Kai! Sanin wane ne wannan mutumin a siyansance, to sai ka matsa kusa dashi sosai.

Zan ci gaba...

Post a Comment

0 Comments