Talla

Matashiya Sadiya Haruna ta kammala Ɗaurin Talala da Kotu Ta Yanke Mata

Daga: Mohd Abdallah
28 Disamba, 2021

KANO, NIJERIYA - Wata kotu ce ta yanke mata hukuncin ɗaurin talala don gyara tarbiyyarta bayan hukumar Hisba ta Kano ta kaddamar da ita gaban ƙuliya bisa zargin yaɗa hotunan tsiraici.

Matashiyar ta shahara sosai a kafafen sada zumunta. Sadiya Haruna, ta kammala ɗaurin talala da kotun shari'a da ke Jihar Kano ta yanke mata.

DSP Musbahu Lawan Kofar Nasarawa ne ya tabbatar da haka a wata tattaunawa da aka yi da shi ranar Talata.

Mai shari'a Ali Jibrin ya yanke wa Sadiya Haruna hukuncin ɗaurin talala na wata shida, inda ya yi umarni ta riƙa zuwa makarantar Islamiyya don gyara tarbiyya da sanin yadda za ta riƙa mu'amala a matsayinta na Musulma.

Mai Shari'a Jibrin ya umarci jami'an hukumar Hisbah su riƙa raka ta makaranta sannan su kai masa rajista domin ya tabbatar tana zuwa makaranta.

A watan Agusta ne rundunar Hisbah ta kama matashiyar bisa zargin yaɗa hotunan batsa a shafukkan sada zumunta. 

Ta taba rubutawa a shafinta na Instagram,

Let's ne @queen_sadi_skincare na Maiduguri 🥰 I need a cute sugar dady that I will spoil him with my cuteness 🤪 🏃‍♀️🏃‍♀️🏃‍♀️

Wato, 

Mu haɗu a @queen_sadi_skincare na Maiguduri Ina neman wani kyakyawan Najaddu wanda zan lalata da wannan kyakyawan jikin nawa. 
Bayan sakinta, DSP Musbahu, ya ce 

"A yau wannan baiwar Allah mai suna Sadiya Haruna ta kammala wa'adin ɗaurin talalar da aka yi mata domin koya mata tarbiyya na tsawon watanni shida".

Ya ƙara da cewa,

"Tun lokacin da muka karɓe ta mun sanya ta a makaranta domin ta riƙa koyon tarbiyya, kuma Alhamdulillahi, daga cikin abubuwan da ta koya sun haɗa da tarbiyar kanta da nazarin litattafai da suka haɗa da Alkur'ani da Hadisai."

Matashiyar Sadiya Haruna ta shahara  a shafukkan sada zumunta kamar su Tiktok da Instagram da Facebook da Snapchat da sauransu. Ko a shafin Instagram kaɗai tana da mabiya dubu ashirin. Ta shahara sosai wajen yaɗa hotuna da bidiyo inda wasu ke ganin hotunan da bidiyo da take yaɗawa sun saɓa tarbiyya da kuma al'ada.

Post a Comment

0 Comments