Litattafan Hausa Don Malamai da Dalibai, Za a Iya Sauke PDF ɗin Litattafan a Wayoyin Hannu
Arewa News sun wallafa litattafan Hausa (Primary) 1 zuwa 6 a shafinsu na www.arewanews.org.ng waɗanda za su taimawa Malaman Makarantar Primary wajen koyar da Harshen Hausa. An rubuta wannan litattafai masu suna ‘Hausa Firamare’, Litattafan sun yi daidai da Manhajar Koyarwar Firamare 1 zuwa 6 (Primary Curriculum 2018), zubin litattafan ya yi daidai da Sabuwar Manhajar Hausa wadda Hukumar Bincike da Haɓaka Ilimi ta Nijeriya (NERDC) ta sabunta a shekarar 2018. An sauya sunan litattafan daga ‘Sabuwar Hanyar Koyon Karatu da Rubutu a Hausa’ zuwa ‘Hausa Firamare’ domin samu sauƙi wajen furucin sunan littafin. Za a iya sauke (Download) PDF ɗin litattafan a wayoyin hannu idan aka ziyarci ɓangare Ebooks dake shafin na Arewa News.
0 Comments