Daga: Aminu Abdullahi Muh’d
Ga ta nan, ga ta nanku.
Wata rana Kurege ya je gidan Kura ya
ce, su tafi farautar kayan daɗi a jeji. Kura ta amince. Suka shirya suka kama
hanyar daji.
Da suka isa bakin rafi sai Kura ta
ce, to su rabu a nan. Ta ce, tun da shi Kurege ƙarami ne ya bi cikin ciyawa,
ita kuma Kura da yake babba ce, za ta bi kan hanya. Da fari Kurege ya ƙi yarda,
amma daga baya ya haƙura, ya bi cikin ciyawa yana tafiya har ya kai ga gidan Zuma,
ya tarar ƙudan Zumar suna ciki.
Sai ya saurare su ya ji duk sanda za
su fita sukan ce,
“Buɗe buss,”
Sai ƙofar gidan ta buɗe, su fita.
Idan sun dawu sai su ce,
“Rufe kiff,”
Sai kuma ƙofar gidan ta rufe. Da ya
gane yadda suke yi, sai ya laɓe har ƙudan Zuma suka gama fita. Da ya ga haka
sai ya matsa kusa ya ce,
“Buɗe buss,”
Sai ƙofa ta buɗe. Sai Kurege ya
shiga ya kwashi zuma ya sha, ya cika jakarsa, ya fito, ya dubi ƙofa ya ce,
“Rufe kiff,”
Sai ƙofa ta rufe, ya kama hanya ya dawo
inda suka yi alƙawari za su haɗu da Kura. Ita kuma Kura da ta kama hanyarta, ta
rinƙa tafiya ba ta ga komai ba, ga shi ta fara jin yunwa. Can dai ta hango
zawayi a malale a gindin bishiya, ta je ta kama shan zawo har ta ƙoshi. Daga
nan ta ɗebi sauran zawayin nan ta zuba a Jakarta, ta kama hanyar inda suka yi
alƙawari za su haɗu da Kurege. Da ta iso sai ta tarar ashe Kurege ya riga ta
dawowa. Kurege ya dubi Kura, ya ce,
“Kura ga shi kin ciko jakarki da
kayan daɗi, sai ki ɗan ɗebo mani abin da ki ka samo.”
Da Kura ta ji haka sai ta ƙi, ta ce
ina nashi?
Sai ya ce to zai ɗan ɗebo mata, ita
ma ta ɗebo masa nata, amma idan na Kurege ba daɗi, zai biya ta nata. Kurege ya
yarda. Da Kura ta buɗe jaka sai Kurege ya fara jin warin kashi, ya dubi Kura ya
ce mata ya fasa shan abin data zo dashi. Da ta ji haka, sai ta ce to shi ke
nan, amma ya ɗan bata nasa. Kurege ya buɗe jakarsa ya ɗeba mata, ya ba ta.
Ta ta ji zaƙi sai ta jefar da Jakarta ta kuma ce sai Kurege ya nuna mata inda ya samo wannan zumar. Kurege ya ce to su tafi ya nuna mata. Suka kama hanya, har suka je gidan zuma, ya gaya mata yadda za ta buɗe ƙofar gidan Zuma.
Nan take Kura ta je ta buɗe gidan zuma, Kura ta fara shan zuma har ta ƙoshi, ta cika Jakarta. Amma kuma sai ta manta yadda za ta buɗe ta fita, sai ta rinƙa cewa,
“Rufe kif.”
Ta dai kasa fita har ƙudan Zuma suka
dawo daga cin furanni, suka hau Kura da harbi, duk jikinta ya kumbura. Kurege
ya gudu ya bar ta, daga baya ta koma gida duk fuskarta a kumbure. A gida aka
tambaye ta me ya same ta, sai ta ce,
“Ai na yi yaƙi ne da wasu namun
daji, amma duk na kashe su sai dai jikina ya kumbura.”
Da ta je gidan Kurege sai ya ɓuya, ya ce,
“A gaya mata ba na gida.”
Kura ta ce,
“Idan ya dawo a gaya masa in bakinsa
ya yi masa ƙaiƙayi, to ya daka da dutse kafin mu hadu,”
Sai ta yi tafiyarta.
Ƙurunƙus.
Darussan Dake Cikin Tatsuniyar
·
Natsuwa maganin kuskure.
·
Kwaɗayi mabuɗin wahala.
0 Comments