Kura Da Zomanya
Gat a nan, ga ta nanku.
A can cikin wani ƙungurmin daji
akwai wata Zomanya mai ciki, wadda gidanta yake kusa da na wata Kura, ita ma
mai juna biyu. Suna zaman lafiya da junansu irin na maƙwabta. Wata rana sai Zomanyar
nan ta je wurin Kura ta ce mata,
“Kin ga ni da ke mun kusa haihuwa,
ya kamata mu nemi wurin da za mu rinƙa ɓoye ‘ya’yanmu.”
Sai Kura ta ce,
”E, gaskiya ne, to amma bari mu tona
rami babba domin mu saka ‘ya’yanmu a ciki.”
Da suka tona rami sai suka zauna
tare, har lokacin haihuwar su ya yi. Da suka haihu, sai suka tara ‘ya’yansu a
rami ɗaya, kuma suka yi alƙawari cewa Kura za ta rinƙa samo masu abinci, ita
kuma Zomanya za ta rinƙa rainon ‘ya’yansu. Suka zauna, in Kura ta tafi neman
abinci ta dawo, sai ta miƙa wa Zomanya ta ci, kuma ta raba wa ‘ya’yansu.
Amma ita kuwa Zomanya, in an kawo
mata abinci sai ta ba ‘ya’yanta su ci, in sun ƙoshi sai ta cinye sauran, ta hana
‘ya’yan Kura. Kullum haka, kuma in Kura ta zo ta ce za ta duba lafiyar
‘ya’yanta sai Zomanya ta ce, ai sun ci abinci sun ƙoshi, suna barci.
Haka suka yi ta yi, har dai wata
rana Kura ta ce sai ta ga ‘ya’yanta. Da ta leƙa ramin ta jawo ‘ya’yanta sai ta
ga duk sun rame. Sai ta tambayi ‘ya’yanta abin da ya same su, suka rame haka.
Sai ‘ya’yan suka ce, ai ba a ba su abinci, in an kawo abinci sai Zomanya ta
hana su, ta ba ‘ya’yanta, su kuwa sai ta sa suyi barcin dole.
Da jin haka sai ran Kura ya ɓaci, ta
yi kuka, ta yi gurnani da ƙaraji mai tsanani, ta ce, tun da Zomanya ta ci
amanarta, to ita da ‘ya’yanta za su cinye Zomanya da ‘ya’yanta gaba ɗaya. Ko da
Zomanya ta ji abin da Kura ta faɗa, sai ta rasa abin da za ta yi, idanunta suka
raina fata.
Tsoro ya kama ta. Sai ta dubi Kura ta
ce,
“To shi ken nan, tun da kin ce ni da
‘ya’yana mun zama nama, to ki yi haƙuri mu fito daga rami tukuna.”
Zomanya ta shiga rami ta gaya wa
‘ya’yanta idan ta fita Kura ta bi ta, to su fita da gudu su yi nasu wuri. Da Kura
ta sake magana, sai Zomanya ta haɗa manyan kunnuwanta biyu, ta ɗan miƙo su waje
ta ce da Kura,
“Don Allah ki riƙe mani takalma na
kafin in fito.”
Jin haka sai ya sa ran Kura ya ɓaci,
ita a tsammaninta ya za a yi kamar Zomanya ta ce ta riƙe mata takalma, bayan ta
zama nama a wurinta. Sai ta kama kunnuwan Zomanya da ƙarfi ta finciko su ta
jefar, wai ita a nufinta takalma ne. sai kunnuwa suka sulluɓe, Zomanya da
‘ya’yanta suka ranta a na kare. Kamar wasa, Kura ta kasa kama ko ɗaya daga
cikinsu.
Ƙurunƙus.
Darasin Dake Cikin Tatsuniyar
Hannu ɗaya ba ya ɗaukar jikka.
Ƙarshen maci amana jin kunya.
Kowa ya ci zomo, ya ci gudu.
0 Comments