Talla

Ko Da Gaske ne Ganduje Zai Canza Sheka Daga APC zuwa PRP?

Daga: Hauwa'u Bello
20 Disamba, 2021

KANO, NIJERIYA - Gwamnatin Kano da ke Arewa Nijeriya ta musanta jita-jitar da ake yaɗawa wadda ke cewa Gwamnan Jihar Abdullahi Umar Ganduje da tawagarsa na shirin canza sheka daga jam'iyyar APC zuwa PRP.

An fara yaɗa jita-jitar bayan ganawar da ɓangaren APC na Gwamnan ke yi wajen ƙoƙarin ɗaukaka ƙara kan hukuncin da wata kotu ta yi a Abuja game da zaben shugabanin jam'iyyar a mazaɓu da ƙananan hukumomi na Kano.

Kotun ya yanke hukunci ne a ranar Juma'a inda ta tabbatar da nasara ga ɓangaren Shekarau.

Alƙalin kotun mai shari'a Hamza Muazu wanda ya zartar da hukuncin ya buƙaci ɓangaren Gwamna Ganduje da ya biya Shekarau tarar miliyan ɗaya.

An alaƙanta shirin Gwamnan na sauya sheƙa daga jam'iyyar ta APC sakamakon hukuncin wanda ya ƙara rura wutar rikicin APC a Kano tsakanin ɓangaren gwamnan da na Shekarau.

Kwamishinan raya karkara na Jihar wato Musa Iliyasu Kwankwaso na ɗaya daga cikin jiga-jigan ɓangaren na Ganduje, ya ce,

"Batun canza sheƙa ba shi da wani tushe ballantana makama".

Ya ƙara da cewa,

"Sune suke ƙoƙarin ficewa daga APC ba mu ba, amma Gwamna wanda yake kan kujera ya zai yi haka, an ma kawo Gwamnan da ba a Jam'iyya yake ba kuma da ya shigo ya karɓi jagorancin Jam'iyya, sannan kuma a ce Gwamnan da ke cikin Jam'iyyar zai fice saboda rikici, sune suke shirin ficewa''.

Ya kuma ce,

 ''Jam'iyyar APC ta mu ce, kuma za a ci gaba da ƙoƙarin yin sulhu, domin rikicin siyasa ba sabon abu ba ne kuma za a zo a daidaita idan har waɗanda ke rikicin da su na nan cikin jam'iyyar ba su fita ba''

Wani abu da ke sake fito da rikicin ƙarara shi ne rushe zaɓukan shugabannin mazabu na jam'iyyar wanda bangaren Gwamnatin Jihar ta gudanar da kotu ta yi, bayan shigar da kara da ɓangaren Malam Ibrahim Shekarau ya yi.

An daɗe ana dambarwar siyasa a Jihar Kano, Jihar da take da tsananin tasiri a Arewacin Nijeriya. Gari mafi girma da ƙarfin kasuwanci a Arewacin Nijeriya kuma na biyu a faɗin Nijeriya.

Post a Comment

0 Comments