15 Desamba, 2021
KANO, NIJERIYA - Allah Ya yi wa fitaccen ɗan wasan fina-finan Hausa Sani Garba SK rasuwa a yau Laraba a birnin Kano, bayan ya sha fama da rashin lafiya.
Wani fitaccen furodusa Abdul Amart Mai Kwashewa ne ya bayyana rasuwar ɗan wasan.
Marigayin ya rasu ne a Asibitin Muhammadu Abdullahi Wase da ke Nasarawa a ranar Laraba da yamma.
Amart ya ce,
"Sani SK ya kai kusan shekara uku yana jinya, amma rashin lafiyar ta taso masa sosai ne a baya-bayan nan inda ya shafe mako biyar yana jinya a asibiti"
Amart ya ƙara da cewa,
"Ciwo suga ne yake fama da shi, wacce daga bisani ta haifar masa da cututtuka irinsu ƙoda da hanta da hawan jini".
A baya dai an sha yaɗa jita-jitar rasuwar Sani SK, inda ya dinga musantawa da kansa ma a wasu lokutan.
"A ranar yau da ya rasu ɗinnan aka fara yi masa wankin ƙoda," a cewar Furodusa Amart, wanda shi ke tsaye a kan kula ɗaukar nauyin kula da lafiyar marigayin.
Sani Garba SK ɗan asalin unguwar Zage ne a cikin birnin Kano, kuma a baya kafin ya fara harkar fina-finai mai yabon Manzon Allah ne a ƙungiyar Usha'un Nabiyyu.
Kafin kwanciyarsa a Asibitin Nasarawa sai da ya kwanta a Asibitin Murtala da ke cikin birni.
Abdul Amart ya ce tuni aka tafi da gawar mamacin gida, kuma za a yi jana'izarsa a gobe Alhamis.
Allah ya jiƙansa da rahma
0 Comments