Talla

Nafisa Abdullahi Na cikin Yan Nollywood da Aka fi Nema a Google a Shekarar 2021

Daga: Hauwa'u Bello
19 Disamba, 2021

KANO, NIJERIYA - Nafisa Abdullahi waddan ta shahara a fina-finan Hausa tana cikin jerin taurarin da aka fi neman ƙarin bayani a kansu a shafin Google Search a shekarar 2021 a Najeriya,  Google Search shafi ne da ake bincike da neman ƙarin bayani.

Nafisa ta fito a cikin fina-finan Hausa da dama, amma fin ɗinta na karshe shi ne 'Labarina'. Nafisa ta shiga jerin ne tare da taurarin fim na kudancin Nijeriya da ake kira Nollywood.

A cikin Jerin sunayen taurarin, ita ce ta shida a sashen taurarin fina-finai.

Nafisa ce kaɗai daga taurarin Kannywood da ta shiga cikin taurari 10 na farko da aka fi neman ƙarin bayani a kansu a Google Search.

Rahama Sadau da Fati Washa da Maryam Yahaya da Hadiza Gabon na daga cikin jerin taurarin Hausa waɗanda duka shahara.

Shafin Google kan fitar da kalmomi da sunaye da mutane waɗanda miliyoyin masu amfani da shafin suka fi bincikawa duk shekara.

Shafin Google na yi wa sunayen rukuni, inda ake da rukunan mawaƙa da waƙar da wasanni da 'yan fim da fina-finan da tambayoyin da aka fi yi.

Nafisa na da mabiya miliyan biyu a Instagram da 176,600 a Twitter da kuma wasu miliyan biyu a Facebook.

Post a Comment

0 Comments