Daga: Hauwa'u Bello
ABUJA, NIJERIYA — Shugaban Ƙasar Nijeriya Muhammadu Buhari ya amince da ɗauki sabbin ‘yansanda guda dubu gonaa ƙasar.
Bashir Ahmad ne ya bayyana hakan a cikin wani saƙo da ya wallafa.
Mai taimakawa Shugaban a fannin yaɗa labarai ta kafafen zamani ya ce,
“Shugaba Muhammadu Buhari ya ba da umarnin a ɗauki ‘yansanda guda dubu goma 10,000 a matsayin jami’an ‘yansanda a Jihohi talatin da shidda da kuma babban birnin tarayyar Abuja.”
Ya ƙara da cewa,
An ɗauki wannan mataki don a tunkari ƙalubalen tsaro a wasu sassan ƙasar.”
A cewar sanarwar, za a ɗauki mutum goma a kowace ƙaramar hukuma cikin ƙananan hukumomi 774 da ke Nijeriya, tuni har an sanar da waɗanda suka nemi aikin ta hanyar tura masu saƙon imel.
Ɗaukar aikin yansandan zai taimaka sosai wajen kawo ƙarshen tashe-tashen hankulla da kashe-kashe da satar mutane don karɓar kuɗin fansa. Ƙasar dai na fama da matsalolin rashin tsaro wanda yasa ƴan ƙasa ke barci da ido ɗaya.
Garuruwan Katsina da Kaduna da Zamfara da Sokoto da Kebbi da Niger na fama da matsalolin tsaro inda ɓarayin daji suka addabi waɗannan jahohi, yayinda Jihar Jos ke fama da faɗan ƙabilanci.
A Kudancin Ƙasar kuwa akwai matsalolin ƴan aware masu son kafa ƙasar Biyafara.
0 Comments