Talla

Bello Turji Ya Aika da Wasikar Ban Hakuri Ga Al'ummar Zamfara da Shinkafi

Daga: Hauwa'u Bello
18 Disamba, 2021

ZAMFARA, NIJERIYA - Shahararren Ɓarawon Dajin nan mai satar mutane don karɓar kuɗin fansa wanda aka fi sani da Bello Turji ya rubuta wata wasiƙa wadda a cikinta ya nemi afuwan mutane bisa ta'asar da ya tafkawa. Ɓarawon ya rubuta wasiƙar ne mai shafi uku zuwa ga Masarautar Shinkafi da Gwamnatin Jihar Zamfara da kuma Shugaban Ƙasa wato Muhammadu Buhari. 

A cikin wasiƙar wadda ake hasashen an rubuta ranar 14 ga watan Disamba 2021, an ga kwanan wata da kuma bismillah, sannan ya buɗe da muƙaddama sannan ya rubuta cewa, daga Muhammadu Bello Turji Fakai. Wannan muƙadama da gabatarwa ne yasa ake zargin cewa wasiƙar shi da kansa ne ya rubuta ta.

A cikin wasiƙar Bello Turji ya nemi sulhu kamar yadda aka yi can baya. Sannan a cikin wasiƙar ya bayyana cewa shi ba ɓarawo bane. Bisa wannan yana neman a zauna a tattauna sulhu tsakaninsa da mutane sannan kuma ya nemi a bar Fulani su ci gaba da mu'amala da sauran al'umma kamar dai yadda ake yi can baya. Ya ce yawan tsangwamar da ake yi wa Fulani ne yasa suka ɗauki makamai, amma yanzu a shirye suke su yi sulhu.

A cikin takardar, ya buƙaci in za ayi zaman, a zauna da malamai irin su Malam Sheikh Ahmad Mahmud Gumi, ya ce ya sanya sunansa ne saboda Malam ya taɓa zuwa yi masu wa'azi kuma sun gamsu da ilimin da ya karantar da su.

 Garuruwan Katsina da Zamfara da Kaduna da Sokoto suna fama da hare-haren ƴan fashi masu satar mutane don karɓar kuɗin fansa. Harin da ya raba mutane da gidajensu. A cikin sati na sama ne Jami'an tsaro suka yi dirar mikiya a dazukan Zamfara da Sokoto. Ko shekaran jiya sai da aka tsinci muryar wani mutum cikin odiyo inda yake bayar da labarin yadda sojoji su ke yin luguden wuta a dazukan da ɓarayin suka ɓoye. Duk da yake dai ba a san sahihancin muryar dake cikin odiyon ba.

Post a Comment

1 Comments

  1. Ai ba wasiƙa ya ka mata ache ya rububa video ya kama ta muga ya Turo saboda kowa yana iya rubutawa ya ce shi ya rubuta ko ya dadi wannan zamanin komi ana iyayi

    ReplyDelete
Emoji
(y)
:)
:(
hihi
:-)
:D
=D
:-d
;(
;-(
@-)
:P
:o
:>)
(o)
:p
(p)
:-s
(m)
8-)
:-t
:-b
b-(
:-#
=p~
x-)
(k)