Daga: Hauwa’u Bello
27 Disamba, 2021
ZAMFARA, NIJERIYA — Wasu mahara sun sace sama da mata 20, bayan wasu hare-hare da suka kai a ƙauyuka 15 da ke yankin babban birnin Jihar wato Gusau.
Mazauna ƙauyukan Geba da Tsakuwa da Gidan Kada da Gidan Ƙaura sun tabbatar da cewa ɓarayin dajin sun shiga ƙauyukan a ranar Asabar, inda suka kashe mazaje tare da kona dukiyoyi, suka kuma sace mata da ‘yan mata waɗanda suka shige da su cikin daji.
Wani ganau ya ce,
A ƙauyen Kura sun sace macce 10 sun tafi dasu, a ƙauyen Bayauri sun sace mace 9, haka kuma sun shiga ƙauye Gana sun ɗauke macce 7, a ƙauyen Duma sun sace mace 7.
Rahotanni sun ce mutane da dama sun fara barin ƙauyukansu suna yin hijira, mafi yawan masu yin gudun hijirar suna tafiya Gasau ne.
Kwamishinan Yaɗa Labarai na Jihar Zamfara wato Ibrahim Dosara, wanda ya tabbatar da kai jerin hare-haren, ya ƙara da cewa, jim kadan bayan shigar ɓarayin dajin jami'an tsaro sun kai ɗauki.
Ya ƙara da cewa,
Akwai sojoji da ke aiki a yankin, kuma sun kai ɗauki a garin Geba. Lokacin da suka isa mutane uku sun ji rauni kuma sun tarwatsa yan bindigar.
Kwamishinan ya musanta cewa ba a kai wa al'ummar kauyukan sama da 15 ɗauki ba.
Jihohin Katsina da Kaduna da Zamfara da Sokoto da Kebbi na fama da hare-haren ɓarayin daji masu satar mutane don karɓar kuɗin fansa.
0 Comments