Daga: Mohammad Abdallah
30 Disamba, 2021
KATSINA, NIJERIYA - An kashe akalla 'yan bindiga 38 yayin da 'yan sanda biyar suka mutu a samame daban-daban da aka kai cikin jihar Katsina.
Rundunar ƴansanda ta Jihar Katsina ta bayyana cewa, ta kashe ɓarayin daji mutum 38 a wani samame da ta kai maɓoyar ɓarayin, rundunar ta faɗi haka ne a wajen wani taron manema labarai da ya gudana ƙarkashin shugaban ƴansandan Jihar wato Sanusi Buba.
Shugaban ƴandandan ya ce,
Babu shakka wannan shekarar da ta ƙare an fuskanci ƙalubale mai yawa a Katsina musamman na tsaro, sai dai rundunar ƴansandan Jihar ta samu nasarori masu yawa a yaƙin da take da ƴan bindiga da masu satar mutane da ƴan fashi da sauran mutane masu aikata manyan laifuka a cikin Jihar.
Ya ƙara da cewa,
A cikin wannan shekara ta 2021 an samu ragowar aikata laifuka a cikin Jihar
Ya ci gaba da cewa,
A wani samame da Jami'anmu suka kai, an samu nasarar kashe ƴan bindiga talatin da takwas, amma an kashe mana jami'ai biyar.
Rundunar ta ce an kama wasu da ake zargi da aikata muggan ayyuka.
A wani ɓangare kuma, an kama mutune 874 da aka gurfanar gaban shari'a a Jihar waɗanda suka aikata laifuka daban-daban.
Garuruwan Katsina da Kaduna da Zamfara da Sokoto da Kebbi na fama da hare-haren ɓarayin daji masu satar mutane don karɓar kuɗin fansa.
0 Comments