Arewa News
16 Disemba, 2021
KANO, NIJERIYA - Rundunar 'yan sandan Jihar Kano ta kama wasu da take zarginsu da aikata miyagun laifuka a Jihar.
Kwamishinan 'yan sandan Jihar, Sama'ila Shu'aibu Dikko ne ya sanar da hakan a wani taron manema labarai da rundunar ta kira a Hedikwatarta da ke unguwar Bompai a jiya ranar Alhamis 16 ga watan Disambar 2021.
Kwamishinan ya ce,
"A samamen da jami'an 'yansanda ƙarƙashin rundunar Puff-Adder suke kaiwa, mun yi nasarar kama mutum 245 da ake zargi da aikata miyagun laifuka waɗanda suka haɗa da: Fashi da makami, da satar mutane, da ɓarayin shanu, da ɓarayin motoci, da ɓarayin waya da 'yan daba, da masu ta'ammali da miyagun kwayoyi. Tuni aka gurfanar da wasu daga cikin masu laifin gaban shari'a domin fuskantar sakamakonsu".
Kwamishinan ya faɗi jerin adadin waɗanda aka kama da kuma zarge-zargen da ake masu. Ya faɗi cewa an kama, 'Yan fashi da makami 38 da masu satar mutane 9 da ƴan damfarar internet 12 da ɓarayin shanu 72 da ɓarayin motoci 25 da ɓarayin adaidaita sahu 12 da masu ta'ammali da miyagun kwayoyi 17 da 'Yan daba 118, bayan waɗannan ƴansandan sun kuɓutar da mutum 6 da aka yi garkuwa da su.
Haka kuma an kama bindiga 35, ciki har da AK47 da bindiga samfurin SNG. Haka kuma, an samu motoci 26 da adaidaita sahu 14 da kekuna 14 da wuƙaƙe 92 da goruna da na'urar kwamfuta 4 da wayoyin salula 54 da injin janareto 50.
An kama tabar wiwi moli 303 da kwayar taramadol da ta kai naira miliyan 9 da kwayar rafanol takarda 140 da walabe 150 na maganin tari mai sinadarin Kodin da sukudai kwalabe 44 yida kuma shanu 66. Ƴan sandan sun yi wannan samame ne daga farkon watan Nuwamba zuwa Disambar 2021.
Kwamishinan 'yan sandan, ya yi kira ga al'ummar Jihar Kano da zarar sun ga wani abu da ba daidai ba, ko suka ga wani mutum marar gaskiya su sanar da ofishin 'yan sanda mafi kusa, ko su kira lambobi kamar haka: 08032419754, 08123821575, 08076091271, haka kuma hukumar ta samar da manhaja mai suna "NPF Rescue Me" da za a iya saukewa a wayoyin hannu.
0 Comments