19 Disamba, 2021
ABUJA, NIJERIYA - Rundunar 'yansanda ta Nijeriya ta ce ta kama wasu da ta kira gawurtattun masu garkuwa da mutane guda goma sha ɗaya a Jihar Taraba da ke tsakiyar Nijeriya tare da ƙwace makamai da yawan gaske.
Wata sanarwa da rundunar ta fitar a yau Lahadi ta ce mutanen suna da hannu a hare-hare da dama, ciki har da satar wani jami'in hukumar kwastam da wani ɗan uwan sarkin Jalingo da kuma ɗansanda mai muƙamin Sajan, ɓarayin sun yi garkuwa da mutanen ne a Garin Jalingo.
Kakakin 'yan sanda Frank Mba ya ce,
"Dakarunmy sun yi nasarar ƙwace bindiga tara, ciki har da AK-47 guda bakwai, da ɗumbin harsasai da ƙwayoyi lokacin da suka kai samame.
Ya ƙara da cewa,
"Kamen waɗanda ake zargin ya biyo bayan tura rundunar gaggawa ta Intelligence Response Team zuwa Taraba domin taimaka wa 'yansandan Taraba wajen kawo ƙarshen satar mutane cikin gaggawa".
Sanarwar ta zargi biyu daga cikin mutanen da hannu wajen kashe wani ɗansanda da kuma raunata wani a wani hari da suka kai, inda suka yi garkuwa da wasu mutane.
Garuruwan Katsina, Kaduna, Sokoto, Zamfara, Niger da Taraba na ɗaya daga cikin garuruwan dake fama da hare-haren ɓarayin daji masu satar mutane don karɓar kuɗin fansa.
0 Comments