Daga: Hauwa’u Bello
19 Disamba, 2021
KANO, NIJERIYA — Wata Kotu a Unguwar Hotoro dake Birnin Kano Arewacin Nijeriya ta saurari ƙarar da aka shigar kan jarumin Kannywood Sadiƙ Sani Sadiƙ, ƙarar dai na zargin jarumin da yin kane-kane bisa kuɗin wani Mutum mai suna Aliyu Muhammad Hanas. An dai samu rasiɗin biyan kuɗi na shigar da ƙara mai ɗauke da sunan Aliyu Muhammad wanda ya biya kuɗin shigar da kara a ranar 11 da watan Nuwamba, 2021. A jikin rasiɗin akwai sunan Sadiƙ Sani Sadiƙ a matsayin wanda ake ƙara.
Malam Aliyu Darakta ne kuma Furodusa a masana’antar Kannywood, ya shigar da ƙara a kan Jarumin, inda ya ce yana bin jarumin kuɗi masu yawa, wanda jarumin yaƙi ya biya waɗannan maƙudan kuɗi. Kodayake Jarumin Sadiƙ Sani Sadiƙ ya sha yin alƙawarin biyar kuɗin, amma bai samu damar biya ba, kuma daga baya sai ya bar ɗaukar Lambar wayar Daraktan. Daraktan ya yi zargin cewa, jarumin ya karɓar masa kuɗi da niyar yi masa aikin fim, amma sai ya ƙi zuwa wajen da ake ɗaukar fim ɗin.
Malam Aliyu ya ce,
“Na tuntuɓi Sadiƙ kan wani fim da nake so ya fito, wanda na shirya, mun yi ciniki da shi, na bashi kuɗin da ya buƙata, sai aka samu matasala, bai zo wajen shirin fim ɗin ba, dole na ɗaga lokaci amma bai zo ba, daga bisani na nemi Ali Nuhu wanda shi ne ya maye gurbi Sadiƙ. Bayan nan sai na nemi ya dawo mani da kuɗin da na bashi amma sai ya yi ta mani wasa da hankali”
Malam Aliyu ya ƙara da cewa,
“Akwai lokacin da na samu labarin yana cikin Shoprite Kano, na ɗauki Yansanda muka tafi don hukuma ta shiga tsakaninmu, a lokacin ne ya ba Maje El-hajeej Hotoro kaɗan daga cikin kuɗin ya kawo mani”
Wasu furodusoshi sun yi ƙoƙarin shawo kan lamarin, kamar Usman Mu’azu da Suleiman Abubakar da Alassan Kwalli lamarin da ya ci tura. Dole dai aka shiga kotu domin a samu sasanci tsakanin mutanen biyu.
0 Comments