16 Desamba, 2021
ABUJA,
NIJERIYA - Ƙasar China ta ce za ta tura tawaga ta musamman ta ƙwararru kan
binciken laifuka domin tattaunawa da hukumomin tsaron Najeriya.
Jakadan
ƙasar China a Najeriya Cui Jianchun ne ya sanar da hakan a ranar Laraba inda ya
ce China za ta yi haka ne saboda ta damu sosai a kan matsalolin tsaron da Nijeriyar
ke fuskanta.
Mista
Cui ya bayyana cewa wannan yunƙurin da China ke yi yana daga cikin dubban goyon
bayan da take ba ƙasar wajen magance matsalolin tsaro, ya kuma ƙara da cewa ya
ce, nan ba da daɗewa ba ƙwararrun za su zo ƙasar Najeriyar don fara aikin
binciken matsalolin da suka addabi ƙasar na rashin tsaro.
Ko
a cikin watan nan, saida wasu ɓarayi suka kashe tare da ƙona mutane ashirin da
uku a Jihar Sokoto, lamarin da ya ja hankalin duniya inda mutane daga Arewa
suka yi ta zanga-zangar lumana da kiraye-kiraye ga gwamnati a ɗauki mataki a
kan rashin tsaro.
0 Comments