ABUKA, NIJERIYA - Zainab Aliyu, matashiyar nan da a shekarar 2019 ta shafe watanni a tsare a kurkukun Saudiyya bisa zargin safarar miyagun ƙwayoyi, ta zama jami'ar hukumar yaƙi da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta Najeriya, NDLEA.
An sako Zainab ne daga kurkukun Saudiyya a ranar 30 ga watan Afrilun 2019 bayan an gano cewa ba ta da laifi wasu ne suka yi mata sharri.
A yanzu matashiyar, mai shekara 25, ta kammala karɓar horo a Kwalejin horas da jami'an hukumar ta NDLEA da ke Katon Rikkos a jihar Filato da ke Najeriya.
Bayan kammala karɓar horon, ta fito da anini ɗaya a matsayin 'Assistant Superintendent of Narcotics'.
Zainab ta kammala karatun digirinta daga Jami'ar Yusuf Maitama Sule da ke Kano ta taɓa zama muhimmin batu a Najeriya a lokacin da ake ta fafutikar ganin an sako ta.
Zainab ta shafe watanni huɗu a gidan yarin Jeddah a inda a nan ne aka yanke mata hukuncin kisa, bayan nan ne hukumomin Najeriya ƙarƙashin jagorancin ministan shari'a Abubakar Malami suka yi ƙoƙarin ganin an sako ta.
Daga baya hukumar NDLEA ta kama wasu ma'aikata a filin jirgin Malam Aminu Kano da ke Kano waɗanda su ne ake zargi da saka mata ƙwayoyin a cikin kayanta haka kuma ba ta san an saka mata ƙwayoyin ba har sai bayan da aka kamata.
Mahaifinta Habib Aliyu ya yi godiya ga Allah bayan ƴarsa ta samu wannan aiki da Hukumar NDLEA a yayin wata hira da BBC.
Yar uwarta Hajara ita ma ta shaida cewa suna matuƙar alfahari da Zainab bisa wannan mataki da ta kai a yanzu.
A yayin yaye sabbin jami'an hukumar ta NDLEA wanda aka yi a jihar Filato a ranar Juma'a, shugaban hukumar Buba Marwa ya yi gargaɗi ga sabbin jami'an kusan su 2,000 da kada su yarda masu safarar miyagun ƙwayoyi su yaudare su da kuɗi su kuma tabbatar sun yi aikin su yadda ya kamata.
0 Comments