Talla

Musa Bello: Masari Ne Ya Sanya Mani Son Yin Takara

1 Nuwamba, 2021
KATSINA, NIJERIYA -  Ba zan nemi kowane irin mukami ba, tunda Aminu Bello Masari yayi Governor,  ni gurina ya cika, haka Muntari Lawal, Chief of Staff, ya fadamin da bakinshi,

Irin wannan amsar SGS ya bani sadda ake rade radin zaiyi takarar Governor a 2019, lokacin da ya turani adaukeni aiki a Isah Kaita College of Education, Dutsinma, sannan banyi Masters Degree!

Lokacin da mai Girma Governor, Rt. Hon.Aminu Bello Masari ya iskeni a class, Government Science Sec.Sch. Dutsinma, da marece, sadda ya kai wata ziyarar bazata, ina koya 'Political apathy' .........

Daga cikin tanbayar da yai mani, yace gashi kana koyama yara kada su kyamaci siyasa, 'to kai kana da sha'awar siyasar, amsar da na bashi, ita yanzu zan tabbatar ma shi

Na manta, Speaker na wancan lokacin, Aliyu Sabi'u Muduru, ya lallabo ta baya yace mani, "kai baka rokonshi komai" sai nace mashi lokacin na zuwa, to ban sani ba ko lokacin ne yayi yanzu!

Don haka zanyi takarar dan majalisar jiha, kamar yadda alokacin na nuna mashi, sha'awata ga siyasar

Allah yai mana zabi mafi alheri, duk abinda ke alheri Allah ya tabbatar dashi, ko muna so ko bamu so ya Allah, madamar shi ne alheri.

Post a Comment

0 Comments