29 Nuwamba, 2021
Sabon jirgin yaƙin rundunar sojin Nijeriya na Super Tucano ya tarwatsa mayaƙan ISWAP tare da lalata motocinsu na igwa a garin Gajiram da ke Jihar Borno.
Mayaƙan sun shiga garin a cikin motocin yaƙi da zummar kai hari, daga bisani sai jirgin yaƙin ya isa wajen.
Rundunar sojin Nijeriya ta ce ta ƙwace makamai da dama a hannun Mayaƙan dagaa bisani kuma dakarun sama da na ƙasa suka fatattaki mayaƙan.
Kafar sadarwa ta PRNigeria ta ce wani jami'in leƙen asiri na soja ya ce a ƙalla an ga gawa 26 na mayaƙan bayan hare-haren.
Ta ƙara da cewa,
"Zuwa yanzu mun ƙirga gawa 26 na ƴan ta'addan amma abin takaici mun rasa sojoji biyu a lokacin da suke faɗa".
A watan Yuli ne Najeriya ta karɓi jiragen yaƙi samfurin Super Tucano da ta saya a hannun Amurka da nufin yaƙi da matsalar rashin tsaro a Arewa maso gabashin ƙasar da sauran sassan da ke da irin wannan matsala.
0 Comments