Talla

Hikayata 2021: Aishatu Musa Dalil ce gwarzuwar gasar

Daga Hafiz Adam Koza
ABUJA, NIJERIYA - Daliba a Sashen Koyar da Ingilishi da Faransanci, Jami'ar Umaru Musa Yar'aduwa Katsina, Aishatu Musa Dalil, ita ce gwarzuwar gasar Hikayata a wannan shekarar ta 2021.
 Hikayata gasa ce da sashen Hausa na BBC ke shiryawa ga mata marubuta Hausa a kowace shekara tun daga 2016 kawo yau da aka bayyana gwarzuwar ta 2021. A'isha Dalil 'yar asalin jihar Kaduna ce wadda ta kasance mafi ƙarancin shekaru a cikin zarata uku da suka sami nasara a bana. 
Ga jerin sunayen gwarazan da suka yi nasara a mataki na farko da shekarun nasararsu da kuma jihohin da suka fito:
1. 2016 – A’isha Mohammed Sabitu ( Aisha Mobil Mobil ) daga jihar Katsina.
2. 2017 – Maimuna Idris Sani Beli  daga jihar Kano.
3. 2018 – Safiyya Jibril Abubakar daga jihar Kaduna.
4. 2019 – Safiyya Ahmad daga jihar Kaduna.
5. 2020 – Maryam Umar  daga jihar Sakkwato.
6. 2021 – Aishatu Musa Dalil daga jihar Kaduna.

Post a Comment

0 Comments