Talla

Gwamna Ganduje: Muna nazari kan hukuncin kotu na biyan Sarki Sanusi II diyya

1Disamba, 2021
KANO, NIKERIA - Gwamantin Jihar Kano ta ce, tana nazari a kan hukuncin da wata babbar kotu da ke birnin Abuja ta yanke ta biya tsohon Sarki Kano Muhammadu Sanusi na II diyyar Naira Miliyan 10 haka kuma ta nemi gafararsa bisa korarsa daga Jihar.

Kwamishinan shari'a na Kano Barista Musa Lawan ya ce,
 
"Gwamnati za tayi nazari kan hukuncin kotun, za ta san mataki na gaba da za ta dauka"

Ya ƙara da cewa,

" Mun sa lauyoyinmu su nemi kundin shari'ar domin mu yi nazari mu duba shi, don mu san ko za mu ɗaukaka ƙara?". 

Ya ce, kundin tsarin mulki ya ba su dama su duba su gani idan kotu ta yi hukuncin da ya dace a kansu.

Sai dai gwamnatin jihar Kano ta ce Sarki Mihammadu Sanusi na II ba shi ne sarki na farko da aka kora daga kasar Hausa a tarihi ba.

"Ita dai kasar Hausa kasa ce mai tarihi da yawa, kuma kowa ya san cewa tarihi ya nuna cewa duk wani sarkin da aka cire ko ya sauka da kansa shi ne ya ke fita daga kasar".

Ya ce, akwai Sarakuna da aka ɗauke su aka kai su wani gari, don haka duk wani sarki da aka cire ya kamata ya girmama masaurauta.

Wasu na ganin cewa ya kamata a ba sarkin da aka cire damar zabar garin da ya ke son ya koma da zama.

Muhammadu Sanusi na II bai kalubalanci sauke shi daga kan mulki ba, amma ya nemi kotun ta bayar da umarni a sake shi daga tsarewar da aka yi masa a wancan lokacin da kuma dawo masa da 'yancinsa na kasancewarsa ɗan adam.

Ya nemi kotu ta hana waɗanda ya kai ƙara tsangwamar sa da kuma keta hakkinsa na ɗan adam.

Sai dai kotun ta ce korar da gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje ta yi wa tsohon Sarkin na Kano daga jihar ya saɓa ƙa'ida kuma haramtacce ne.

Post a Comment

0 Comments