Fri, Nov 19, 2021.
Daga: Jamil Sauwa-Sauwa, Mun ɗauko daga shafinsa na Fesbuk
ABUJA, NIJERIYA - Abin dana ƙaru dashi, daga cikin littafin "Allah Make Us" mai ɗaukar ma'anar; "Haka Allah Ya Yi Mu" idan an fassara zuwa Hausa, wanda ya yi magana kan Ƴan Daudu, ba zai wuce amsar ta su wa ne Ƴan Daudu ba, wannan rubutu.
Ƴan Daudu: wasu mutane ne daga jinsin maza, masu kwaikwayon jinsin mata, wato a iya cewa; masu maida kansu mata, ta hanyar kwaikwayon yanayin halittar da mata suke, ta maganarsu, tafiyarsu, shigarsu [sutura], rawarsu, amfani da sunansu da kuma wasu daga cikin ɗabi'o'i ko salo na jinsin mata wanda ba a san jinsin maza da su ba. Wanda hakan ya saɓawa al'ada ta malam Bahaushe a wajan tarbiyya, al'adar riƙo da addini na musulunci, mutunci, ladabi da kuma kunya wanda su ne sinadaran gina tarbiyya da kuma ɗabi'ar Bahaushe, haka Tada (gargajiyanci) na Bahaushe wanda ya gada daga iyaye da kakanni. Dangantakarsu da Hausawa bata wuce ta hanyar alaƙarsu da Ƴan Bori a fagen biki, inda suke zuwa wajan bikin wasan Bori a yi dasu, wanda kuma shi Bori; yana daga cikin gargajiyar jahiliyya [maguzanci] ta Hausawa, sunan kansa "Daudu" ko "Ɗan Daudu, ya samo asali daga sunan wani iska [aljani ko kurwa] na Bori, kamar yadda Rudolf Pell Gaudio, ya kawo a cikin littafinsa, a iya ce wa ta nan "Ƴan Daudu" sunan ya sami asali, suka sami suna daga "Daudun Bori", wannan itace alaƙarsu da Bori da kuma Hausawa. Ƴan Daudu, ba a iya cikin Hausawa, suka fito ba, suna da mutane kala-kala cikinsu daga ƙabilu daban daban da muke dasu a Najeriya, haka garuruwa, wasu daga wasu ƙasashen ƙetare na Najeriya suke, irinsu Chadi, Nijar, Kamaru dss, bariki ta haɗa su.
Sun bayyana tsakiyar ƙarni na ashirin (20s) da kuma bayan mulkin-mallaka na turawa garemu, suna kama da turawa ta hanyar "gay" wato "maza masu neman maza" ko "ƴan luɗu" wanda su kuma sun bayya a ƙarshen ƙarni na sha-tara (19s) zuwa farkon ƙarni na ashirin (20s) , a iya cewa; sun samu wannan ɗabi'a ko koya daga turawa, su kuma turawa da sauran masu wannan ɗabi'a sun gajeta daga mutanen annabi Luɗu, wanda Al-ƙur'ani ya labarta mana su da kuma aikinsu na yadda suke; namiji ya zakewa ɗan uwansa namiji saɓanin mace, haka su Ƴan Daudu kishiyoyi ne ga Ƴan Maɗigo su ne; jinsin mata da suke neman junansu, wanda a yaren Ƴan Daudu suke kiransu da Ƴan kifi.
Mawaƙi Aliyu Aƙilu, yana cewa; cikin waƙarsa mai taken Ƴan Daudu, daya wallafa a shekara ta 1976 cikin littafinsa mai taken Fasaha Aƙiliya;
-Af! jama’a, ku bari in waigo,
In taɓa ɗan rakiyar ta Makwalla.
-Shin kuwa ko kun lura da shi dai,
Ko in fallashi jakin mata?
-Can wani shashashan daga gefe,
Wofin wofiyo, banzar banza.
-Domin in nuna shi a fili,
Har ma ai masa kallon banza.
-Ɗan-hamsin yake, ko Ɗan Daudu?
Wa ma zai kula garar kashi?
-Ba shi a tsuntsu, ba shi a dabba:
Jemage shi ke, mai ban haushi.
-Babu fikafikkai gun dabba;
Tsuntsu shi kuwa ba shi haƙori.
-Shi dai ya zama jakin-doki,
Ya ɓata wa mazaje suna.
-Ya ƙi mafi girman darajar tasa:
Shi ya zaɓi ta ƙarshen baya.
-Da ninki biyu ce daraja tasa:
Ya watsar, ya riƙe falle ɗai.
Wasu na kallon Ƴan Daudu;masu bin maza;wasu kuma da masu yin kalwancin;wasu kuma da masu kwaikwayon mata, kowa da irin idon da yake kallonsu, ta dalilin yadda suke, duk da ba duka suka zama ɗayaba wajan yin aiki ko kuma yanayi, duba da rabe-rabensu da kuma dalilai ko nufi da suke dashi na shigar su Daudu ko zama Ƴan Daudu. Ƴan Daudu, tamkar bishiya suke mai rassa da yawa, kowanne reshe da irin ganyensa.
Akwai Ƴan Daudu umuman a suna, haka a rabe-rabe, irin su Ƴan Daudun riga, Ƴan Daudu fararen hula ko Ƴan Aras ko Harka, haka akwai kuma Ƴan Kano-Jidda. Duka wannan a cikin Daudu suke, kuma kowanne akwai yadda suke da kuma halinsu, ɗabi'unsu na yau da kullum kana da aikinsu. Su Ƴan daudun riga; su ne wanda a ɓoye suke daudunsu, idan suka fito cikin mutane suna sajewa tamkar yadda ko wane namiji yake, domin kunya da gudun tsangwama da kyarar mutane garesu. Ƴan daudu fararen hula; su ne masu yin harka, wato Ƴan aras maza masu neman maza tamkar yadda karuwai suke. Su kuma Ƴan Kano-Jidda; su ne wanda daudunsu har ƙasashen ƙetare suke zuwa musamman daga Kano, masu zuwa Saudiyya, suna aikinsu na daudu da kuma tarayya da Larabawa domin samin kuɗi.
Wajejen rayuwarsu baya wuce bariki, kasuwa, tashar mota suna yiwa ma'aikata da matafiya abinci, da kuma gidajen mata masu zaman kansu [karuwai] suna kawalci ko kuma zaman kansu suma suna samun masu zuwa nemansu. Haka wajajen biki da bori.
Duka suna yin haka ne ko wasu da sunan sana'a domin samun kuɗi duba da hali na rashi da talauci da suka tsinci kansu a rayuwa, shi yasa wasu basa harka ko kuma su zama fararen hula suna mu'amala ta aras. Wasu kuma suna yi ne kawai domin sheɗanci. Allah ya shirya. Wasu suna yin daudu a gafe guda kuma suna da iyalansu, matansu na aure da ƴaƴansu suna rayuwa, sau da yawa irin waɗannan sun ɗauki harkarsu da sunan sana'a.
Suna da yaruka da a junansu suka san ma'anarsu, wanda suke kira da yaren harka, misalin ire iren lafuzan yarensu su ne kamar haka; harka [luwaɗi], masu harka [maza masu neman maza], mai ƙoƙo [mace], su meka ko ashi suna ga ƴan daudu [masu yin harka], ɗan aras [na-miji wanda ba ɗan daudu ba mai bin na-miji ko wanda ya bi na-miji], su kalmar; lemo [gaba] sai kuma kalmar; birni [dubura], su fararen hula [maza masu neman maza], su mai ido [ƴan daudu masu harka], da makaho ko garwa [ga mutanen da basa harka], duk wannan suna daga cikin kalmomin da suke amfani dasu. Haka kuma suna da habaici da karin magana, misali; "ke banza! Ɗinkin kasuwa. Yaushe ne? Ake ba ki takarda muke dariya muka ta hana ki tafiya.", "aikin banza! Agwagwa tura ta cikin ruwa.", da kuma su "balbela ci da motsin wani". Haka zagi; shegiya, ƴar iska dss.
A nahiyar kuma mu'amala tsakaninsu da junansu; su na son junansu, ta hanyar sada zumunta tsakaninsu tare da girmama juna da mu'amala mai kyau, ta wannan hanyar suke ruɗar wasu. Haka yadda suke kiran junansu babba ya kira na ƙasa dashi da sunan "ƙanwata" ƙarami da kai na sama dashi har matsayin uwatai, wanda kuwa suke soyayya tsakaninsu zaka ji sunaye kala-kala, irin su ; "matata", "budurwata" dss.
A idon jama'a ko al'ummar gari, su abin ƙyama ne, tare da gudu da ala-tur da halinsu. Shi yasa suke shan tsangwama, tsana da ƙiyayya, ta dalilin haka da yawansu ba sa iya zama a garin da aka sansu ko suka taso duba da kallon da ake musu da sunan marasa tarbiyya da kunya, makamai na rusa tarbiyyar bi'ar al'ummar gari da lalata.
Ƙarshesu ko kuma na ce fara ɓacewarsu daga cikin al'umma, yana da alaƙa da abubuwa guda biyu;
1- Zuwan cutar Ƙanjamau a shekara ta 1982 da kuma yaɗuwarta cikin lardin Sudan [Afirka] ƙarshen ƙarni na 20 da farkon ƙarni na 21, wanda ta zama guguwar tashin kasuwar bariki, wanda ta yi sanadiyyar mutuwar karuwai da Ƴan Daudu da dama da saka tsoro cikin zukatan ƴan bariki.
2- Kafa shari'ar musulunci a arewacin Najeriya a 1999, da kuma bazuwarta sassa na jihohi da dama a 2000 dake arewa, shari'a ta taka rawa wajan kawo ƙarshen bariki da ƴan bariki irin su Ƴan Daudu dss. A dalilin shari'a su ka yi ta hijira suna barin garuruwan da ta yi ƙarfi izuwa marasa ƙarfi wanda irin ƙungiyoyi na Hisba basu yi tasiri garesu ba, ko ni a ta dalilin irin waɗannan gari na san Ƴan Daudu ko na ce na taɓa ganinsu, lokacin da nake ɗalibin Sakandiri a garin Haɗejia wajejen 2010, inda suke da wajan dafa abinci a tashoshi da wasu wajaje a cikin gari.
Zan ƙarƙare da waƙen A Aƙilu;
- Ɗan daudu wawa, maras mafaɗi,
Ka tuba ga Allah, ka bar maguɗi,
Shi ne fa kanwa, uwar ƴan haɗi,
Ka bar ɗaura gyauto, kana yafa shuɗi,
Ka zam sanya riga, kana yin naɗi.
- Allahu shi ya hallice ka namiji,
Ka bar ɓata kanka kana hardaji,
Da ɗai namiji bai zama mace, ka ji,
Kaza mace ba ta zama namiji,
Da ɗai tsamiya ba ta daidai da gamji.
0 Comments