Talla

Davido: zai ba gidajen marayu kyautar naira miliyan 250

20 Nuwamba, 2021
ABUJA, NIJERIYA - Davido ya ce zai ba gidajen marayu da ke Najeriya kuɗi har naira miliyan 25,  daga cikin kuɗin da magoya bayansa suka aika masa.

Mawaƙin ya nemi magoya bayansa da su tura masa da kuɗi zuwa wani asusun ajiya da ke ɗauke da sunansa.

A ranar Asabar ce Davido ya ce ya gabatar da kokon barar cikin raha, amma yawan waɗanda suka amsa kiran nasa ya zarce yadda ya yi tsammani.

Ya godewa waɗanda suka ba da gudunmmawar kuɗi, ya bayyana yadda za a yi amfani da su.

Zai bayar da wani ɓangare na kuɗin ga gidajen marayu wanda magoya bayansa suka aike masa da kuma gudunmmawar naira miliyan hamsin da wani ya bayar.

Ana yi wa Davido kallon ɗaya daga cikin manyan shahararun mawakan Afrika.

Ya taɓa samun lambar yabo ta MTV da BET kuma ya yi aiki tare da wasu shahararun mawaƙan ƙasashen waje da suka haɗa da Chris Brown da Nicki Minaj.

Bukatar da ya gabatar ta kafofin sada zumunta ta janyo ra'ayoyi mabanbanta daga masu bibiyarsa.

Wasu sun ce mawaƙin mai magoya baya miliyan 22 a shafin Instagram a wasu lokutan ya na son ya nuna yadda yake rayuwar kasaita a shafin intanet.

A wani sakon daya wallafa a shafin Twitter, Davido ya ce manufarsa ita ce ya tara kuɗi domin ya samu damar shigo da motarsa ta Rolls-Royce daga tashar jirgin ruwa.

Ya tura da bayanan asusun ajiyar kuɗi na banki tare da rarraba hotuna, adadin kuɗin da ke ciki ya ci gaba da ƙaruwa a 'yan kwanaki.

A sanarwar da ya fitar ranar Asabar mawaƙin ya ce manufarsa ita ce ya ga tara wannan kudi a zagayowar ranar haihuwarsa a kowace shekara domin taimakawa alumma.

Ya ce, "Ni mai son taimakawa mutane ne".

Post a Comment

0 Comments