Daga: Bello Hamisu Ida
18 Desamba, 2021
KATSINA, NIJERIYA - Zazzaɓin Lassa wata cuta ce da ta samo asali daga wani gari da ake kira Lassa a Jihar Borno, cutar na yaɗuwa ne a duk wani abu da ɓera ya samu kusantarsa, musamman abinci. Alamomin cutar sun haɗa da zafin zazzaɓi, ciwon kai, da amai (haraswa). hanyoyi da ake kamuwa da cutar sun haɗa da ajiyar kayan abinci ba tare da kulawa da su ba wanda hakan ke bai wa ɓeraye damar lalata abinci.
A duk lokacin da mutane suka ajiye abubuwan amfaninsu, akwai buƙatar sake tsaftace su kafin amfani da su don guje wa kamuwa da cutar. Duk lokacin da ɓera ko gafiya suka yi fitsari ko kashi a cikin abinci, kuma aka ci abinci, ko cin naman ɓera da sauran namomin dabbobin daji, to akwai yiwuwar kamuwa da cutar ba tare da ɓata lokaci ba.K
wayar cutar na yaɗuwa ne ta hanyar tu'ammali da abinci da kuma kayayyakin amfanin gida da suka gurɓata da fitsari da kashin ɓera ko kuma ta hanyar shafar duk wani ruwa-ruwa daga jikin mutum da ya kamu. Shan garin kwaki ma yana kawo kamuwa da cutar zazzabin Lassa.
A ɗauki matakin garzayawa zuwa asibiti da zaran sun fara jin wani canji a jikinsu ko dai na ciwon kai da zazzaɓi ko in an ga ƙuraje a cikin jiki. Hukumar ta NCDC da sauran hukumomin lafiya sun kafa kwamitoci dake da wakilai daga hukumar lafiya ta duniya da sauran masu ruwa da tsaki domin shawo kan cutar zazzaɓin lassa. Bincike dai ya nuna cewa cutar zazzabin Lassa tafi yawaita a lokacin zafi kuma cutar tayi tsanani ne a Najeriya a shekara ta dubu biyu da sha takwas.
Cutar ta kashe mutum kusan sittin a Najeriya inda ta bazu zuwa jihohi goma sha tara da suka ƙunshi na kudu da arewacin ƙasar. Cibiyar takaita yaɗuwar cutuka ta ƙasar ta ce, zazzaɓin ta ƙara bazuwa zuwa jihohi irinsu Kaduna da Benue da Kwara da Rivers.
Sauran jihohin da ke fama da cutar sun haɗa da Oyo da Ondo da Kogi da Bauchi da Enugu da Nasarawa da Ebonyi da Filato da Taraba da Adamawa da Gombe da Imo da Delta kuma Abuja. Cibiyar ta ce kusan mutum ɗari uku aka tabbatar suna ɗauke da cutar. Cutar wadda ɓeraye ke haddasawa na ƙara sanya damuwa a tsakanin hukumomin lafiya na ƙasar.
Lassa na da kamanceceniya da cutukan Ebola da Marburg inda take haddasa zazzabi da haraswa idan kuma ya yi tsanani sai maras lafiya ya fara zubar da jini.
1.
Daga wane gari aka fara samun cutar Lassa?
2.
Lissafa dalilai uku da ke haddasa cutar Lassa?
3.
A ƙalla, mutum nawa suka mutu sanadiyar cutar Lassa?
4.
Waɗanne jahohi cutar Lassa ta fi yaɗuwa?
5.
Waɗanne jahohi ne cutar Lassa bata yawaita ba?
6.
Cike waɗannan guraben:
7.
Cutar na yaɗuwa ne a duk wani abu da
8.
Hukumar ta NCDC da sauran hukumomin lafiya
0 Comments