10 Oktoba, 2021
ZAMFARA, NIJERIYA — Jami’an tsaro dake aikin fatattakar ɓarayi a dazukan Zamfara
sun koka saboda rashin alawus. Jami’an sun yi zargi cewa, sama da wata takwas
kenan aka shafe ba tare da an basu kuɗin alawus ba.
Jami’an sun yi zargin cewa, an jibge su a dazuka da
shigayen tsaro suna fama da walaha da matsalolin rayuwa, kullum hankalinsu a
tashe na abinda gobe zata bayar, kullum idonsu biyu suke kwana don su kare
rayukan al’umma da dukiyoyinsu, amma ba a basu haƙƙinsu.
Kodayake, wani ɗansansan ya ce bayan ƙura ta kai bango, an basu naira dubu ashirin wanda bata yi masu amfanin
komai ba. Mafi yawan Yansanda dake cikin dajin suna haɗa kuɗaɗe ne idan buƙata ta taso domin su
share wa kansu hawaye.
Yansandan suna kira ga hukumomin Jiha zuwa Tarayya
da su duba wannan matsala da suke ciki. Saidai Jihar Zamfara inda Yansandan
suke jibge ta tsame kanta daga wannan magana wadda ta yi zargin cewa jami’an
tsaro basu samun alawus ɗinsu ba har na tsawon
wata takwas.
Honarabul Ibahim Dosara wanda shi ne Kwamishinan yaɗa labarai na Jihar Zamfara ya yi ƙarin bayani, inda ya ce,
gwamnatin Jihar Zamfara ita ce ke biyansu alawus a kowane wata. Ya ce, a bisa
tsarinsu, duk sanda ɗansanda zai fita aiki a
kowace rana to yana da dubu ɗaya, idan aka haɗa a duk wata alawus ɗinsa zai zama dubu
talatin.
Ya ƙara da cewa,
“Muna da shaidar cewa ana bawa kowanne ɗansanda da ya yi aiki a Zamfara alawus ɗinsa, domin duk wanda aka
ba kuɗi sai ya sanya hannun a samar takarda wanda ke nuna shaidar cewa ya karɓa”
Kwamishinan ya yi ƙarin bayani, cewa hukumar
Yansanda ake ba kuɗin don ta basu, kuma yana
da tabbacin cewa ana basu.
Garuruwan Sokoto, da Katsina da Zamfara da Kaduna
dai na fama da hare-haren Yan bindiga da satar mutane don karɓar kuɗin fansa, kuma mafi yawan
waɗanda ake zargi da aikata wannan laifi duk Fulani ne.
Wannan, da ma wasu labarai a biyo mu a shafin
www.arewanews.org.ng
0 Comments